Sama da mutane 4, 000 su ka dawo Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi

Sama da mutane 4, 000 su ka dawo Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi

- Manyan Jam’iyyar SDP da-dama sun sauya sheka daga Jam’iyyar a a Jihar Kebbi

- Jam’iyyar APC mai mulki tayi babban kamu a Garin Shanga da ke Jihar ta Kebbi

- Fiye da mutum 4000 su ka fice daga Jam’iyyar SDP su ka koma APC mai mulki

Sama da mutane 4, 000 su ka dawo Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi

Manyan ‘Yan SDP sun sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC mai mulki
Source: Depositphotos

Mun samu labari cewa manyan jam’iyyar adawa ta SDP sun sauya sheka zuwa APC a cikin karamar hukumar Shanga da ke jihar Kebbi. Hakan na zuwa ne yayin da ake daf da gudanar da babnan zabe a fadin Najeriya.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kebbi, Alhaji Bala Kangiwa ne ya karbi wadanda su ka sauya-shekar. Akalla mutane 4000 ne su ka fice daga jam’iyyar SDP a jihar Kebbi, inda su ka koma APC kamar yadda mu ka ji labari jiya.

KU KARANTA: Mutanen Marafa za su yi watsi da taron da Buhari zai shirya a Zamfara

Manyan APC sun karbi tsofaffin ‘yan jam’iyyar ta SDP ne a wani katafaren dakin taro da ke Garin Birnin Kebbi. Wadanda su ka sauya-shekan, sun bayyana cewa irin ayyukan gwamnatin APC ta sa dole su kayi biyayya su ka bi APC.

Shugaban SDP gaba daya na karamar hukumar Shanga, Abdullahi Shanga da kuma Sakataren sa watau Umar Sawashi, da manyan ‘ya ‘yan jam’iyyar wanda su ka haura 4000 sun bayyana cewa za su yi wa APC aiki a zaben bana.

APC tayi murna da wannan labari inda ta bayyana cewa za a ba kowa dama ya wanke allon sa. Alhaji Shanga ya tabbatar da cewa za su yi bakin kokari wajen ganin Muhammadu Buhari da Abubakar Bagudu sun ci zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel