Daga gidan yari, tsohon gwamna Dariye ya nemi yan Najeriya su zabi Buhari a 2019

Daga gidan yari, tsohon gwamna Dariye ya nemi yan Najeriya su zabi Buhari a 2019

Yayin da yan siyasa ke cigaba da gudanar da yakin neman zabensu, shi kuwa wani tsohon gwamna kira yayi ga al’ummar Najeriya dasu tabbata sun sake zaban shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu don cigaba da kyawawan ayyukan da yake yi.

Legit.ng ta ruwaito tsohon gwamnan jahar Filato, Sanata Joshua Dariye ne ya aika ma yan Najeriya da wannan sako daga dakinsa dake kurkukun Kuje, inda aka daureshi shekaru goma sha hudu sakamakon sata da barnatar da kudin al’umma.

KU KARANTA: Anyi artabu tsakanin mayakan Boko Haram da Sojojin Najeriya a Yobe

Daga gidan yari, tsohon gwamna Dariye ya nemi yan Najeriya su zabi Buhari a 2019

Buhari
Source: UGC

Wannan sako na Dariye ya riski yan Najeriya ne a ranar Litinin, 4, ga watan Feburairu a yayin yakin neman zaben gwamnan jahar Filato, Simon Lalong daya gudana a garin Shendam, inda ya nemi jama’an Filato su tabbata sun zabi Buhari, kuma sun zabi Lalong.

Shugaban jam’iyyar APC reshen jahar Filato, Dabang Letep ne ya isar da sakon Dariye, inda yace Dariye ya umarceshi ya bayyana ma jama’an Filato cewa Buhari da Lalong sun taka rawar gani, don haka akwai bukatar su sake zabensu.

Shima da yake nasa jawabin, Gwamna Lalong na jahar Filato ya yi kira ga kwamitin yakin neman zabensa dasu tabbata sun kiyayi zage zage da cin mutunci. “Dole ne mu tsaya akan ayyukan da muka yi, dole ne mu rungumi zaman lafiya fiye da duk wata bukatar kanmu.

“Gwamnatin ta yi ayyuka masu muhimmanci a jahar nan, wanda muke ganin sun isa su sa jama’a su sake bamu damar mulki a zango na biyu. Kuma akwai bukatar sake zaben shugaba Buhari domin bashi karin shekarun gudanar da aiki.” Inji Gwamna Simon Lalong.

Daga karshe daraktan yakin neman zaben Gwamna Simon Lalong, Pam Dung Gyang ya bayyana godiyarsa ga dubun dubatan jama’an da suka taru a gangamin yakin neman zaben, inda yace hakan tabbaci ne dake nuni ga nasarar da jam’iyyar APC za ta samu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel