Sarkin Musulmi ya yi kira ga Musulmai su fara neman watan Musulunci

Sarkin Musulmi ya yi kira ga Musulmai su fara neman watan Musulunci

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya yi kira ilahirin Musulman Najeriya dasu fita neman sabon watan Musulunci na Jumada Thani daga ranar Talata, 5 ga watan Feburairu.

Sultan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin ganin wata, Farfesa Sambo Junaidu ya fitar a ranar Litinin, 4 ga watan Feburairu wanda yayi daidai da 28 ga watan Jumada Ula shekara 1440 bayan Hijira.

KU KARANTA: Anyi artabu tsakanin mayakan Boko Haram da Sojojin Najeriya a Yobe

Sarkin Musulmi ya yi kira ga Musulmai su fara neman watan Musulunci

Sarkin Musulmi
Source: UGC

Cikin sanarwar, mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi kira ga Musulman Najeriya dasu nemi sabon watan Jumada Thani mai kamawa daga ranar Talata wanda shine yayi daidai da 29 ga watan Jumada Ula.

“Muna kira ga al’ummar Musulmai da cewa Talata 5 ga watan Feburairu it ace daidai da 29 ga watan Feburairu na watan Jimada Ula shekara 1440 bayan Hijira, don haka shine ranar da za’a fara neman sabon watan Jumada Thani 1440.

“Da wannan muke kira ga duk wanda yayi dace da ganin watan daya gaggauta kai rahoto ga dakaci ko hakimi mafi kusa domin a aika da rahoton zuwa ga mai alfarma Sarkin Musulmi.” Inji Farfesa Sambo.

Daga karshe Sultan yayi addu’ar Allah Ya taimaki Musulmai wajen gabatar da ayyukan addininsu cikin sauki, tare da neman Allah Ya shiryi shuwagabannin Musulmai da mabiyansu gabaki daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel