Anyi artabu tsakanin mayakan Boko Haram da Sojojin Najeriya a Yobe

Anyi artabu tsakanin mayakan Boko Haram da Sojojin Najeriya a Yobe

Dakarun runduna ta 159 na rundunar Sojin kasa dake aikin tabbatar da tsaro a yankin Arewa maso gabas mai taken Operation Lafiya Dole sun yi artabu da wasu gungun mayakan rundunar ta’addanci ta Boko Haram a jahar Yobe.

Legit.ng ta ruwaito Sojojin sun yi karanbattan ne yayin da yan ta’addan suka yi kokarin kutsa kai cikin wani kauye dake kan iyakar Najeriya da kasar Nijar, kauyen Kanama a cikin karamar hukumar Yunusari ta jahar Yobe.

KU KARANTA: Saraki ya janye karar daya shigar da Buhari akan bahallatsar tsohon Alkalin Alkalai

Anyi artabu tsakanin mayakan Boko Haram da Sojojin Najeriya a Yobe
Sojoji
Source: UGC

Mukaddashin mataimakin daraktan watsa labaru na rundunar Sojan kasa, Laftanar Njoka Irabor ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a garin Damaturu, babban birnin jahar Yobe.

“Da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Litinin ayarin mayakan kungiyar ta’addanci sun yi kokarin kutsa kai cikin kauyen Kanama, inda suka bude wuta a wani hari na mai kan uwa da wabi.

“Nan da nan dakarunmu suka taresu, kuma suka mayar da wuta, ana aka fara musayar wuta, sai dai yan ta’addan sun ji ba dadi, sakamakon taron dangin da Sojojin kasa da Sojojin sama suka yi musu, wanda hakan yasa muka kashe da dama daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere da raunuka a jikinsu.

“A yanzu haka Sojojinmu sun kaddamar da farautar sauran yan ta’addan ruwa a jallo ta hanyar bin sawunsu zuwa iyakan kasar Nijar, zamu fitar da karin bayani game da adadin yan ta’addan da muka kashe tare da makaman da muka kama.” Inji shi.

A wani labari kuma, Babban hafsan Sojan kasa, laftanar janar Tukur Yusuf Buratai ya baiwa dakarun Sojin Najeriya umarnin murkushe kungiyar rajin kafa kasar Biyafara, IPOB daga doron kasa bayan samun wasu bayanan sirri dake nuna kungiyar na kokarin tayar da hankali a yayin zaben 2019.

Buratai ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Litinin, 4 ga watan Feburairu a shelkwatar Sojan kasa, inda yace rundunar Sojan kasa na aiki hannu da hannu da rundunar Yansanda da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da jama’a sun kada kuri’unsu cikin lumana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel