Duk abin da aka yi Buhari sai ya doke Atiku a zaben 2019 – inji Femi Adesina

Duk abin da aka yi Buhari sai ya doke Atiku a zaben 2019 – inji Femi Adesina

Mun samu labari a jiya cewa shugaba Muhammadu Buhari yayi tir da ayyana nasarar ‘dan takarar babbar jam’iyyar PDP mai adawa watau Alhaji Atiku Abubakar da wasu manyan mayun Najeriya su kayi.

Duk abin da aka yi Buhari sai ya doke Atiku a zaben 2019 – inji Femi Adesina

Fadar Shugaban kasa tayi magana bayan Mayu sun ce Atiku zai ci zabe
Source: Facebook

Shugaban kasar na Najeriya ya maida martani ne ta bakin babban mai ba sa shawara da kuma taimaka masa kan harkokin yada labarai, Femi Adesina. Adesina ya kara tabbatar da cewa Atiku Abubakar zai sha kasa a zaben bana.

Mista Femi Adesina yace duk da kungiyar manyan Mayun Najeriya sun hanga sun ga cewa Atiku zai samu nasara a zaben shugaban kasa da za ayi, hakan ba zai hana shugaba Muhammadu Buhari ya samu galaba a kan sa a zaben ba.

Babban hadimin shugaban kasar yayi magana ne game da nasarar da wasu ke hangowa Atiku Abubakar na PDP bayan an ji cewa wasu manya a fadin kasar nan har da kuma Mayu su na ganin ‘dan takarar PDP ne zai ci zaben 2019.

KU KARANTA: Wani Gwamnan Kudu ya nemi mutanen sa su zabi PDP a 2019

Femi Adesina ta shafin sa na sadarwa na zamani na Tuwita ya rubuta cewa, idan rikakkun Mayun kasar nan sun ga dama su daga hannun Atiku, sai dai duk wannan ba zai hana sa faduwa zabe a hannun ‘yan Najeriya a zaben 2019 ba.

Kungiyoyin nan na Afenifere na kasar Yarbawa, da Ohanaeze Ndigbo ta Inyamurai, da kuma manyan Arewa a karkashin NEF da kuma kungiyar PANDEF ta Neja Delta da mutanen tsakyar Najeriya sun ce su na tare da Atiku a 2019.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, shi ma ya bayyana cewa wannan taron dangi da ake yi ba zai hana shugaba Muhammadu Buhari ya zarce a kan ragamar mulkin Najeriya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel