An ci, an sha, and koshi yayin da Buhari ya karbi bakoncin yan majalisa a Villa

An ci, an sha, and koshi yayin da Buhari ya karbi bakoncin yan majalisa a Villa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakoncin yan majalisun wakilai da suka fito daga jam’iyyar APC, tare da sabbin halastattun yan takarar jam’iyyar dake neman wakiltar al’ummomin mazabunsu a majalisar ta hanyar lashe zaben watan Feburairu 2019.

Legit.ng ta ruwaito baya ga tattaunawar da aka yi tsakanin shugaban kasa Buhari da bakinnasa, Buharin ya shirya musu kayatacciyar liyafar cin abinci, inda suka ci, suka sha, suka kuma koshi, daga nan aka watse kowa ya kama gabansa.

KU KARANTA: Saraki ya janye karar daya shigar da Buhari akan bahallatsar tsohon Alkalin Alkalai

An ci, an sha, and koshi yayin da Buhari ya karbi bakoncin yan majalisa a Villa

Villa
Source: Facebook

Shugaban jam’iyyar APC, kuma tsohon gwamnan jahar Edo, kwamared Adams Oshiomole ne ya jagoranci yan majalisun zuwa taron daya gudanar a fadar shugaban kasa a daren Litinin, 4, ga watan Feburairu.

An ci, an sha, and koshi yayin da Buhari ya karbi bakoncin yan majalisa a Villa

Buhari
Source: Facebook

Sauran sun hada da babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, mataimakin kaakakin majalisar wakilai, Yusuf Lasun, shugaban masu rinjaye, Femi Gbajabiamila, kammala cin abincinsu keda sai suka sanya labule da shugaba Buhari inda suka yi gemu da gemu.

Duk da yake babu wani rahoton daya bayyana game da batutuwan da Buhari ya tattauna da yan majalisun, amma alamu sun nuna tattaunawar ba za ta wuce wanda ta danganci zaben 2019 ba.

An ci, an sha, and koshi yayin da Buhari ya karbi bakoncin yan majalisa a Villa

Yan majalisa
Source: Facebook

Idan za’a tuna ko a ranar 28 ga watan Janairu shugaba Muhammadu Buhari yayi kwatankwacin wannan ganawa da Sanatocin jam’iyyar APC, da kuma sabbin halastattun yan takarar Sanata daga jam’iyyar ta APC.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel