Anyi wa 'yan Kwastam bore a Kano, har da kone-kone

Anyi wa 'yan Kwastam bore a Kano, har da kone-kone

- Wani jami'in kwastam ya samu munanan raunuka sakamakon harin da yan sumogal suka kai musu

- A watan da ya gabata ne wani jami'in ya rasa ransa sakamakon mugun gudun da wani Dan sumogal keyi inda yabi ta kanshi

- Shugaban hukumar na ofishin Kano/Jigawa yace bazasu lamunci ire iren cin kashin nan ba

Anyi wa 'yan Kwastam bore a Kano, har da kone-kone

Anyi wa 'yan Kwastam bore a Kano, har da kone-kone
Source: UGC

Wani jami'in kwastam mai aiki da ofishin Kano/Jigawa ya samu raunika sakamakon karon batta da akayi tsakanin jami'an da masu sumogal din shinkafa.

A wani jawabin mai magana da yaun ofishin a jiya, Danbaba yace maharan sun kona motar sintiri guda daya.

"Jami'an mu zasu dau mataki akan wasu da ake zargin yan sumogal din shinkafa ne, sai hatsari ya faru a kusa da inda jami'an ke aiki. Da yan hukumar tsaron hadurra suka isa gurin, sai suka bukaci taimakon jami'an mu don kai wadanda sukayi hatsarin zuwa asibiti mafi kusa,"

"Suna cikin maganar ne yan sumogal dinmu suka yi kansu cewa sune suka jawo hatsarin," inji shi.

GA WANNAN: Kuyi magudi da APC kuyi bayani bayan zabe - PDP ta gargadi INEC

A ranar 30 ga watan janairu ma wani da sumogal ya kashe jami'in hukumar kwastam sakamakon mugun gudun da yake.

Shugaban hukumar kwastam ofishin Kano/Jigawa wanda ya bayyana hakan a jiya, yace bazasu lamunci ire iren wadannan abubuwa da yan sumogal kewa jami'an su ba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel