Sanatan APC zai shirya gangamin yakin neman zabe daban domin Buhari

Sanatan APC zai shirya gangamin yakin neman zabe daban domin Buhari

- Kwanan nan ake sa rai za a shirya taron yakin neman zaben Buhari a Zamfara

- Magoya bayan Kabiru Marafa dai za su kauracewa wannan taro su shirya wani

- Wadanda ke tare da Sanatan jihar za su shirya gangamin na su na APC na dabam

Sanatan APC zai shirya gangamin yakin neman zabe daban domin Buhari

Rikicin Marafa da Yari ta kai za a banbanta taron Shugaba Buhari
Source: Depositphotos

Mun samu labari a farkon makon nan cewa wasu ‘yan taware a jam’iyyar APC mai mulki a Zamfara sun sha alwashin shirya taron yakin neman zaben APC na zaben 2019 na musamman dabam da ainihin taron da jam’iyyar za ta gudanar.

Bangaren Sanata Kabiru Marafa na jam’iyyar APC mai mulki tace za ta tsarawa shugaban kasa Muhammadu Buhari taron yakin neman tazarce a jihar Zamfara. Wani daga cikin Magoya bayan Sanatan ya bayyana hakan.

KU KARANTA: Jiga-jigan APC sun lallabi Majalisar dokoki game da tsige Ambode

Wani Matashi wanda ke cikin tafiyar siyasar Sanata Marafa mai suna Rabiu Abubakar ya fadawa mutanen sa cewa za su shirya gangami na APC daban domin nemawa shugaba Buhari goyon-bayan jama’a a zabe mai zuwa na 2019.

Rabiu Abubakar yayi wannan jawabi ne a wani gidan rediyo inda ya nemi mutanen sa su yi watsi da taron da gwamnatin Zamfara za ta shiryawa Buhari. Abubakar ya nemi magoya bayan Marafa su kauracewa babban taron da za ayi.

Yanzu dai ana ta rikici tsakanin wasu kusoshin jam’iyyar APC a Zamfara da kuma gwamna mai shirin barin-gado Abdul’Aziz Yari wanda yake neman kakaba ‘dan takarar sa. Kabiru Marafa yana cikin manyan masu fito-na-fito da gwamnan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel