Mai masoya da yawa: Dan takarar gwamna a jam'iyyar adawa yace mabiyan sa su zabi Buhari

Mai masoya da yawa: Dan takarar gwamna a jam'iyyar adawa yace mabiyan sa su zabi Buhari

A yayin da zabukan gama gari na shugaban kasa, 'yan majalisar tarayya da kuma gwamnoni da 'yan majalisar jahohi ke cigaba da karatowa, yanayin siyasar na cigaba da zafafa tare da daukar sabon salo kala-kala, 'yan siyasa na cigaba da bayyana ra'ayoyin su.

A yayin da ake cikin hakan ne muka samu labarin cewa dan takarar kujerar gwamnan jihar Zamfara a daya daga cikin jam'iyyun adawa ta All Progressives Grand Alliance (APGA) mai suna Alhaji Sani Shinkafi yace mabiyan sa su zabi shugaba Muhammadu Buhari.

Mai masoya da yawa: Dan takarar gwamna a jam'iyyar adawa yace mabiyan sa su zabi Buhari

Mai masoya da yawa: Dan takarar gwamna a jam'iyyar adawa yace mabiyan sa su zabi Buhari
Source: Twitter

KU KARANTA: Daga Hannun Ganduje: Kwankwaso ya aikawa Buhari sako

Kamar dai yadda majiyar mu ta kamfanin dillacin labaru na Najeriya ya bayyana mana, dan takarar yayi wannan furucin ne a garin Bungudu, karamar hukumar Bungudu yayin cigaba da yakin neman zaben sa ranar Litinin.

Alhaji Sani Shinkafi ya kara da cewa yana sane da cewa jam'iyyar sa ta All Progressives Grand Alliance (APGA) a matakin kasa ta tsayar da dan takarar shugabancin kasa amma shi a matsayin sa na mai hankali, zai yi abun da yake jin ya dace ne ba dole sai jam'iyyar sa ba.

A cewar sa, zai yi anfani da hankalin nasa wajen zabar wanda duk yaga dacewar sa a kowace jam'iyya ya fito ya kuma umurci magoya bayan sa da yin hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel