Shugaba Buhari ya samu goyon baya daga dan takarar gwamna na APGA a Zamfara

Shugaba Buhari ya samu goyon baya daga dan takarar gwamna na APGA a Zamfara

- Alhaji Sani Shinkafi, ya tsayar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari na All Progressives Congress (APC), a matsayin dan takarar Shugaban kasa a zabe mai zuwa

- Sani yace yana sane da cewar jam'iyyarsa ta APGA na da dan takararta na shugaban kasa amma shi Buhari ne zabinsa

- Dan takarar gwamnan yayi alkawarin kawo ci gaba a jihar Zamfara idan har aka zabe shi

Dan yakarar kujerar gwamna na jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) a Zamfara, Alhaji Sani Shinkafi, ya tsayar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari na All Progressives Congress (APC), a matsayin dan takarar Shugaban kasa gabannin zaben 16 ga watan Fabrairu.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Sani ya bayyana hakan ne a Bungudu, hedkwatar karamar hukumar Bungudu da ke jihar, yayin kamfen dinsa.

Shugaba Buhari ya samu goyon baya daga dan takarar gwamna na APGA a Zamfara

Shugaba Buhari ya samu goyon baya daga dan takarar gwamna na APGA a Zamfara
Source: UGC

Ya bayyana cewa: “Ina sane da cewar jam’iyya ta (APGA) na da dan takararta a zabe mai zuwa, amma ina ganin nima ina da yancin yin zabina.

“Don haka ina sanar da cewa zabina shine Shugaban kasa mai mulki a yanzu Muhammadu Buhari sannan ina kira ga yan Najeriya das u sake zabarsa domin ya ci gaba da kyawawan aikin da yake yi kasar.

“Sannan ina kira ga mutanen jihar Zamfara da su zabe ni a matsayin gwamnansu domin na inganta rayuwarsu."

KU KARANTA KUMA: IGP Mohammed ya kawata DIG 7 (cikakken sunaye)

A wani lamari na daban, mun ji cewa mataimakin shugabankasa Yemi Osinbajo a ranar Litininm 4 ga watan Fabrairu yace ko makiyan Shugaban kasa Muhammadu Buhari za su iya bayar da tabbacin cewa shi baya rashawa, inda ya bukaci yan Najeriya da su sake zabarsa a matsayin Shugaban kasa a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu.

Osinbajo ya bukaci yan Najeriya da su guje ma duk wani yaudara na dawo da wadanda ya kira da barayi gwamnati domin kada su sake taba tattalin arzikin kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel