Da duminsa: Mayakan Boko Haram sun yiwa garin Buba Marwa a jihar Adamawa kawanya

Da duminsa: Mayakan Boko Haram sun yiwa garin Buba Marwa a jihar Adamawa kawanya

Wasu 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram na can su na barin wuta a karamar hukumar Michika da ke jihar Adamawa.

Wata majiya ta shaida wa Legit.ng cewar mayakan kungiyar ta Boko Haram sun kai harin garin ne a daren nan.

Tsohon gwamnan jihar Legas a mukin soji, Birgediya Janar Buba Marwa, ya fito ne daga garin Michika.

A yau, Litinin, ne tsohon gwamnan jihar Legas a mulki soji, Birgeiya janar Buba Marwa (mai ritaya) ne ya jagoranci tsofin janar-janar din soji da su ka ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari domin bayyana goyon bayan su ga takarar sa.

Da duminsa: Mayakan Boko Haram sun yiwa garin Buba Marwa a jihar Adamawa kawanya

Mayakan Boko Haram
Source: UGC

Daga cikin tawagar tsofin janar-janar din akwai Navy Capt Caleb Olubolade, tsohon ministan harkokin 'yan sanda lokacin mulkin Jonathan da kuma tsohon shugaban rundunar sojojin ruwa ta kasa, Admiral Jubril Ayinla.

DUBA WANNAN: Shigar Atiku Amurka alfarma ce ta wucin gadi - Rahoton Reuters

Goyon bayan tsofin sojojin na zuwa ne bayan shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamred Adams Oshiomhole, ya ce manyan tsofin janar na soji da ke kasar nan na kulle-kullen kawo karshen gwamnatin shugaba Buhari ta kowacce hanya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel