Shigar Atiku Amurka alfarma ce ta wucin gadi - Rahoton Reuters

Shigar Atiku Amurka alfarma ce ta wucin gadi - Rahoton Reuters

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa wani rahoto da ke bayyana cewar ziyarar da dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya kai kasar kasar Amurka sati biyu da su ka wuce ta yiwu ne saboda an yi masa alfarma ta wucin gadi a kan takunkumin shiga kasar da aka kakaba ma sa shekaru 12 da su ka wuce, kamar yadda masana abinda ya faru su ka tabbatar.

Duk da har yanzu gwamnatin kasar Amurka ba ta ce komai a kan matsayin Atiku ko ziyarar da ya kai kasar ba, ‘yan majalisar kasar Amurka da wasu ma su ruwa da tsaki dangane da ziyarar ta Atiku sun fada wa Reuters cewar Amurka ta haramta wa Atiku shiga kasar saboda hannu da ya ke da shi a wasu laifukan cin hanci guda biyu.

Sai dai a wurin masoya da magoya bayan Atiku, ziyarar da ya kai kasar Amurka a ranakun 17 da 18 ga watan Janairu ta wanke shi daga duk wani zargin cin hanci da ake yamadidin cewar su ne su ka hana shi shiga kasar Amurka na tsawon shekaru 12.

Shigar Atiku Amurka alfarma ce ta wucin gadi - Rahoton Reuters

Atiku a Amurka
Source: UGC

Da yawan manyan jami’an gwamnatin kasar Amurka sun tabbatar da cewar an janye takunkumin da aka saka wa Atiku ne bayan wasu kwararrun ma su iya roko da kulle-kullen siyasa sun shiga sun fita domin ganin cewar an bawa Atiku wata dama ko da kuwa ta wucin gadi ce.

DUBA WANNAN: Zabe: Tsofin Janar 71 sun goyi bayan takarar shugaba Buhari

Wani daga cikin ma su ruwa da tsaki a kan ziyarar ta Atiku da bai yarda a bayyana sunan sa ba ya ce gwamnatin kasar Amurka ta amince ta janye takunkumin na wucin gadi domin ribar da kasar za ta iya samu idan Atiku ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasar Najeriya da za a yi a ranar 16 ga watan Fabarairu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel