Ko makiyan Buhari sun san cewa shi ba barawo bane – Osinbajo

Ko makiyan Buhari sun san cewa shi ba barawo bane – Osinbajo

- Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ko makiyan Buhari za su iya bayar da tabbacin cewa shi ba barawo bane

- Osibajo ya bukaci yan Najeriya da su sake zabarsa a matsayin Shugaban kasa a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu

- Ya shawarci yan Najeriya da kada su yarda a yaudare su wajen dawo da barayin gwamnati kan mulki

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Litininm 4 ga watan Fabrairu yace ko makiyan Shugaban kasa Muhammadu Buhari za su iya bayar da tabbacin cewa shi baya rashawa, inda ya bukaci yan Najeriya da su sake zabarsa a matsayin Shugaban kasa a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu.

Osinbajo ya bukaci yan Najeriya da su guje ma duk wani yaudara na dawo da wadanda ya kira da barayi gwamnati domin kada su sake taba tattalin arzikin kasar.

Ko makiyan Buhari sun san cewa shi ba barawo bane – Osinbajo

Ko makiyan Buhari sun san cewa shi ba barawo bane – Osinbajo
Source: Depositphotos

Yayi magana a fadar Olota na jihar Ogun daga cikin kamfen din neman takarar shugabanci a jihar.

Osinbajo ya alakanta kalubal da karancin ci gaban da ake samu a Najeriya ga rashawa.

KU KARANTA KUMA: Mayu sun tsayar da Atiku bayan tattaunawa da dama a tsaunin Obudu da Zuma

A baya mun ji cewa Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa ba a taba dan siyasa ko ma'aikacin gwamnati da talakawa suka yarda da shi a kasar nan kamar Shugaba Muhammadu Buhari ba.

Gwamnan ya ce 'yan kasar sun san cewa ko a tarihi shugaban kasar bai taba cin amana a mukamai da ayyukan da ya gudanar ba a baya.

El-Rufai wanda ya jadadda hakan a wata hira da manema labarai ya bayyana cewa babu wani dan siyasa da zai iya kayar da dan takarar shugabancin kasar na jam’iyyar APC.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel