Cin hanci: Har yanzu akwai hukumomin gwamnati da ke karkatar da kudin shuga - Buhari

Cin hanci: Har yanzu akwai hukumomin gwamnati da ke karkatar da kudin shuga - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce duk da kokarin gwamnatinsa a bangaren yaki da cin hanci, har yanzu akwai hukumomin gwamnati da basa zuba duk kudaden shiga da su ka samu a asusun gwamnatin tarayya.

"Saba ka'idar aiki domin biyan bukatar kashin kai, nau'i ne na cin hanci. Cin amanar aiki domin biyan bukatar kan mutum ko ta wasu mutane na daga cikin hanyoyin da cin hanci ke kara samun gindin zama. Karkatar da kudin shiga ko na haraji ko kuma amfani da irin wadannan kudade ta hanyar da ta saba wa ka'ida na daga cikin fuskokin cin hanci.

"Na kula cewar duk da kokarin gwamnati na a bangaren yaki da cin hanci, har yanzu akwai hukumomin gwamnati da ke yin kwange wajen saka kudaden shigar da su ka samu. Irin wadannan hukumomi na cigaba da aikata abinda su ka saba yi tamkar ba a samu wani canjin gwamnati ba," a cewar Buhari.

Shugaba Buhari na wadannan kalamai ne yayin rantsar da sabbin mambobin kwamitin gudanarwa na hukumar yaki da cin hanci (ICPC) wanda aka yi a fadar shugaban kasa (Villa).

Cin hanci: Har yanzu akwai hukumomin gwamnati da ke karkatar da kudin shuga - Buhari

Buhari
Source: UGC

A cewar sa, "wannan taro na yau na daga cikin cigaba da yaki da cin hanci da gwamnati na ke yi a kasar nan. Yaki da cin hanci na daga cikin manyan alkawura uku da na dauka kafin na hau mulki kuma har yanzu da nake takara a karo na biyu ina nan a kan kudirina na cigaba da yaki da cin hanci.

"Yaki da cin hanci na da matukar muhimmanci ta fuskar samun cigaba a kasar mu. Hakan ne ya sa nake yawan fadin cewar 'matukar ba mu kashe cin hanci ba, cin hanci zai kashe Najeriya.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya za ta rushe wasu makarantun gaba da sakandire - Ministan Ilimi

"Dukkan mu zamu iya zama shaida a kan irin barnar da cin hanci ya yi ga cigaban kasar mu. Cin hanci ne babbar matsalar da ta hana mu motsa wa domin samun cigaba a kasar mu, kuma shine ya jawo zubewar kima da mutuncin kasar mu.

"Cin hanci ya shiga cikin siyasar mu, tattalin arziki da zamantakewar mu. Ma su adawa da yakin da mu ke yi da cin hanci basu san illolin sa ba ne.

"Amma talakan Najeriya ya san mene ne cin hanci kuma ya san illolin sa. Hakan ne ma ya sa su ke goyon kokarin da mu ke yi wajen yaki da cin hanci da rashawa," a kalaman Buhari.

Shugaba Buhari ya bayyana aniyar sa ta tabbatar da cewar duk hukumomin gwamnati sun zuba duk kudaden haraji da na shiga da su ka shigo hannun su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel