Bidiyo: Jigo a PDP ya yi kira ga mabiyan jam'iyyar su hallaka alkalan zabe

Bidiyo: Jigo a PDP ya yi kira ga mabiyan jam'iyyar su hallaka alkalan zabe

Wata bidiyo ta bayyana a shafin ra'ayi da sada zumunta inda wani da siyasa ya ke magana da babban murya yana kira ga mabiyan jam'iyyarsa su hallaka duk alkalin zaben da ya sanar da sakamakon da basu yarda da shi ba.

Wannan abin takaici ya faru ne a jihar Kaduna inda jigo a jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP ya ke magana a filin yakin neman zaben dan takaran gwamnan jihar, Isa Ashiru Kudan.

Alkaluma sun bayyana cewa wanda yake wannan magana tsohon shugaban jam'iyyar PDP ne mai suna, Alhaji Yaro Makama. Ya yi wannan jawabin ne a gaban dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Isah Ashiru da Sanata Suleiman Hunkuyi kuma.

Isa Ashiru Kudan wanda ya kasance dan majalisan wakilai a gwamnatin baya da Sanata Suleiman Hunkuyi har yanzu basu nisanta kansa daga wannan jawabi da jigon jam'iyyar yayi ba.

Yace: Duk uban da ya tawo ba da sakamako da jama'a suka amince da shi ba, toh billahi lazi ana karban sakamako ana kaishi kabarinshi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel