Tsaro: El Rufa'i zai yiwa sarakunan gargajiya ihsani a jihar Kaduna

Tsaro: El Rufa'i zai yiwa sarakunan gargajiya ihsani a jihar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El Rufa'i, ya sha alwashin yiwa Sarakunan gargajiya na jihar sa kyakkyawan ihsani na biyan su alawus domin sauke nauyin da rataya wuyan su na inganta harkokin tsaro a fadin jihar.

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu cewa, gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El- Rufa'i, ya sha alwashin biyan sarakunan gargajiya alawus domin neman hadin kan su wajen samar da ci gaba ta hanyar inganta tsaro.

Tsaro: El Rufa'i zai yiwa sarakunan gargajiya ihsani a jihar Kaduna

Tsaro: El Rufa'i zai yiwa sarakunan gargajiya ihsani a jihar Kaduna
Source: Depositphotos

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, domin neman hadin kai tare da kara karfin gwiwa da hobbasan Sarakunan gargajiya wajen yakar miyagun ababe na ta'addanci a jihar Kaduna, gwamna El- Rufa'i ya mike tsaye wurjanjan domin yiwa masu rawani ihsani a fadin jihar.

A ranar Asabar din da ta gabata ne Mallam Nasir ya bayar da shaidar hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar, inda ya ce ma'aikatar kula da harkokin kananan hukumomi ta jihar za ta shimfida tsare-tsaren yadda alawus din sarakunan zai kasance.

KARANTA KUMA: Rashin kafa tubalin hadin kai na jam'iyyar PDP zai sanya Atiku ya sha kasa a jihar Legas - Ogunwele

Ya ce tsare-tsaren ma'aikatar zai kayyade adadin kudi da kowane mai daurin rawani zai samu ka ma daga Dagatai, Mai gari da kuma masu Unguwanni domin kara masu karfin gwiwa wajen inganta tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'ummar su.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, gwamna El-Rufa'i ya kuma jaddada kudirin sa na samar da ingatattun makarantu, kyawawan cibiyoyin kiwon lafiya, samar da tsaftaccen ruwan sha da kuma samar ta tabbatacciyar wutar lantarki cikin dukkanin manyan kauyuka da ke fadin jihar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel