IGP Mohammed ya kawata DIG 7 (cikakken sunaye)

IGP Mohammed ya kawata DIG 7 (cikakken sunaye)

Sufeta Janar na yan sanda, Adamu Mohammed a ranar Litinin, 4 ga watan Fabrairu ya kawata sabbin manyan jami’an yan sandan da aka yiwa Karin girma kwanan nan ciki harda mataimakan sufeto janar na yan sanda (DIG) su bakwai tare da sabbin matsayinsu.

An tattaro cewa ba tare da bata lokaci ba aka shigar da su cikin tawagar hukumar rundunar.

Wata sanarwa daga kakakin yan sandan, ACP Frank Mba, ya tabbatar da cewa an tura sabbin jami’an kawata da aka kawata tare da sabbin mataimakan sufeton yan sandan zuwa sabbin sashi.

IGP Mohammed ya kawata DIG 7 (cikakken sunaye)

IGP Mohammed ya kawata DIG 7 (cikakken sunaye)
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: Mayu sun tsayar da Atiku bayan tattaunawa da dama a tsaunin Obudu da Zuma

A cewar Mba, sunayen sabbin jami’an da aka kawata da ofishinsu sun hada da:

1. DIG Usman Tilli Abubakar, sashin kudi da gudanarwa

2. DIG Abdulmajid Ali, sashin ayyuka

3. DIG Frederick Taiwo Lakanu, sashin dabaru da wadatar da kayayyaki

4. DIG Anthony Ogbizi Michael, sashin bincikn masu laifi da kwararru

5. DIG Yakubu Jubrin, sashin horo da ci gaba

6. DIG Aminchi Baraya, sashin bincike da tsare-tsare

7. DIG Godwin Nwobodo, sashin bayanai da sadarwa.

Sufeto Janar na yan sandan ya bukaci mataimakan nasa da su tabbatar da cancantarsu da kwazonsu akan wannan sabbin matsayin da suka hau.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel