Hotuna: Bayan tsallake rijiya da baya, farfesa Osinbajo ya samu sabuwar jirgi daga kamfanin Caverton

Hotuna: Bayan tsallake rijiya da baya, farfesa Osinbajo ya samu sabuwar jirgi daga kamfanin Caverton

Mataimakin shugaban kasa, Farsesa Yemi Osinbajo, ya samu sabuwar jirgi mai saukar angulu daga kamfanin jiragen Caverton.

Wannan aya bayyana ne a wata sako da kamfanin ta daura a shafin sadarwar Tuwita inda ta jaddada kokarinta wajen kare rayuwan mataimakin shugaban kasan.

Tace: "Domin cigaba da nuna jajircewanmu wajen kare rayuwa da ingancin aiki, mataimakin shugaban kasa, farfesa Yemi Osinbajo, zai cigaba da yakin neman zabensa da jirgin Caverton."

Mun kawo muku rahoton cewa jirgi mai saukar angulu wanda ya dau mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo, sanata Ojudu, mataimakin shi na musamman da liktan matar shi ya rikito daga sama.

Hadarin ya faru ne a garin Kabba, jihar Kogi.

Kamar yadda mataimakin nashi na musamman ya fada: "Jirgin mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo ya rikito a garin Kabba amma shi da duk wadanda ke cikin jirgin na lafiya. Yana cigaba da al'amuran shi da ya tsara na yau a jihar Kogi."

Tuni an kaddamar da bincike kan abinda ya sabbab faduwan jirgin mataimakin shugaban kasan. Sakamako na farko ya nuna cewa yanayi ne musabbabin hadari.

Masana ilimin jirgi da masu sharhi kan al'amuran yau da kullum sun karyata wannan magana inda sukace wajibi ne a zurfafa bincike cikin wannan al'amari.

Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjinawa mataimakinsa kan irin jaruntan da ya nuna wajen wannan fitina da Allah ya kawar masa. Ya bayyana hakan ne a wata wasika na musamman da ya rubuta masa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel