Buratai ya bada sabon umarni ga Sojoji game da masu rajin kafa kasar Biyafara

Buratai ya bada sabon umarni ga Sojoji game da masu rajin kafa kasar Biyafara

Babban hafsan Sojan kasa, laftanar janar Tukur Yusuf Buratai ya baiwa dakarun Sojin Najeriya umarnin murkushe kungiyar rajin kafa kasar Biyafara, IPOB daga doron kasa bayan samun wasu bayanan sirri dake nuna kungiyar na kokarin tayar da hankali a yayin zaben 2019.

Buratai ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Litinin, 4 ga watan Feburairu a shelkwatar Sojan kasa, inda yace rundunar Sojan kasa na aiki hannu da hannu da rundunar Yansanda da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da jama’a sun kada kuri’unsu cikin lumana.

KU KARANTA: Saraki ya janye karar daya shigar da Buhari akan bahallatsar tsohon Alkalin Alkalai

A dalilin haka ne Buratai ya sanar da kirkiran wani sabon aiki da Sojoji zasu gudanar mai taken ‘Operation Safe Conduct’, wanda aka shiryashi domin tabbatar da an gudanar da zaben 2019 cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

“Mun samu labarin wasu kungiyoyin marasa kishin kasa dake samun tallafi daga kasashen waje suna shirin tayar da zauni tsaye a wasu sassan kasarnan yayin zaben 2019 dake karatowa, haka zalika muna sane da cewa kungiyar IPOB na cigaba da gudanar da shirye shirye na karkashin kasa don bata zaben.

“Don haka zamu murkushesu ba tare da wata wata ba, domin mu dakatar da duk wasu kulle kullen da suka shirya game da zaben, bugu da kari akwai bukatar hadin gwiwa tsakanin manyan kwamandoji game da rikicin jahar Taraba da wasu jihohi domin a kwantar da rikicin.” Inji shi.

A wani labarin kuma dakarun rundunar Sojin Najeriya na 118 da na 119 sun aika da wasu gungun mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram su hudu zuwa barzahu bayan wata zazzafar arangama data faru a garin Malam Fatori, dake kan iyakar Najeriya da Chadi.

Wannan lamari ya faru ne a daren Asabar, 2 ga watan Janairu a cikin karamar hukumar Abadam ta jahar Borno, yayin da mayakan suka yi kokarin kutsa kai cikin garin Malam Fatori da nufin kaddamar da hare hare.

Sai dai kamar yadda masu iya magana ke cewa, kifi na ganinka mai jar koma, ashe dakarun Sojin runduna ta 118 da ta 119 suna kallonsu, inda nan take suka taresu, suka dinga antaya musu luguden wuta, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar yan ta’adda guda hudu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel