Hukumar Hisbah ta kama almajirai 228 a Kano cikin watan Janairu

Hukumar Hisbah ta kama almajirai 228 a Kano cikin watan Janairu

- Hukumar Hisbah reshen jihar Kano Fabrairu ta bayyana cewa ta kama mabarata 228 a watan Janairun 2019

- An kama su ne akan zargin saba doka na haramta bara a unguwannin jihar

- Kakakin hukumar ya bayyana cewa mafi akasarin mabaratan na da nakasa ciki harda makafai

Hukumar Hisbah reshen jihar Kano a ranar Litinin, 4 ga watan Fabrairu ta bayyana cewa ta kama mabarata 228 a watan Janairun 2019, kan zargin saba doka na haramta bara a unguwannin jihar.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Adamu Yahaya, ya bayyana hakan a wani hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Kano.

Hukumar Hisbah ta kama almajirai 228 a Kano cikin watan Janairu

Hukumar Hisbah ta kama almajirai 228 a Kano cikin watan Janairu
Source: Depositphotos

Ya bayyana cewa anyi kamun ne a hanyar France Road, Lodge Road, State Road, Gwammaja, Yankaba Bus-stop da gidajen abinci.

“Daga cikin almajiran 228, 73 yan Kano ne yayinda 155 suka fito daga Bauchi, Borno, Jigawa da Zamfara,” inji Mista Yahaya.

KU KARANTA KUMA: Mayu sun tsayar da Atiku bayan tattaunawa da dama a tsaunin Obudu da Zuma

A cewar jami’in, mafi akasarin mabaratan na da nakasa ciki harda makafai.

Ya yi bayanin cewa waanda ba yan Kano bane za a mayar dasu jihohinsu. Sannan kuma cewa yan Kano daga cikinsu an tantance su sannan aka sake su bayan an wayar masu da kai.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel