Saraki ya janye karar daya shigar da Buhari akan bahallatsar tsohon Alkalin Alkalai

Saraki ya janye karar daya shigar da Buhari akan bahallatsar tsohon Alkalin Alkalai

Wani rahoto da muka samu da dumi duminsa ya tabbatar da cewa majalisar dattawan Najeriya a karkashin jagorancin shugaban majalisar, Sanata Bukola Saraki ta janye karar da ta shigar da shugaban kasa Muhamamdu Buhari a gaban kotun koli ta Najeriya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin Saraki, Yusuph Olaniyonu ne ya sanar da haka a ranar Litinin, 4 ga watan Feburairu, inda yace majalisar ta dauki matakin janye karar ne bayan majalisar sharia ta kasa, NJC, ta sanya baki cikin lamarin.

KU KARANTA: Buhari ya rantsar da Farfesa Owasanoye sabon shugaban hukumar ICPC

“Don haka majalisar ta janye karar da ta shigar gaban kotun koli, duk da cewa a gobe Talata, 5 ga wata za’a cigaba da sauraron karar, an dauki wannan mataki ne sakamakon gamsuwa da majalisar ta yi na cewa majalisar sharia ta kasa zata iya shawo kan rikicin.” Inji shi.

A ranar 28 ga watan Janairu ne majalisar dattawa ta shigar da shugaban kasa Buhari kara gaban kotun koli game da sallamar tsohon Alkalin Alkalai, Mai Sharia Walter Onnghen da yayi, inda suka bukaci fassarar kundin tsarin mulkin Najeriya daga kotun kan ko Buhari na da karfin yin hakan ko kuwa?

Haka zalika majalisar dattawa ta nemi kotun ta tabbatar mata da ko shugaban kasa Buhari ya shiga huruminta ta hanyar sallamar tsohon Alkalin Alkalan, kamar yadda sashi na 292 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar.

Sai dai jim kadan bayan shigar da karar da majalisar ta yi gaban kotun koli, sai yayan jam’iyyar APC dake cikin majalisar suka nesanta kansu da wannan mataki, inda suka bayyana cewa wasu Sanatoci yan kalilan a karkashin jagorancin Saraki ne suka shigar da karar, su kam ba da yawunsu ba.

A cikin wata hira da shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya yi da manema labaru bayan shigar da karar, yace, babu yadda za’ayi ace majalisa ce ta shigar da karar bayan bashi da masaniy a matsayinsa na jagoran masu rinjaye, sai dai Saraki yace a karan kansa ya shigar da kara ba majalisa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel