Zabe: Buratai ya gana da GOCs, kwamandoji da manyan sojoji

Zabe: Buratai ya gana da GOCs, kwamandoji da manyan sojoji

Rahotanni da ke zuwa mana sun yi ikirarin cewa Shugaban hafsan soji, Laftanal-Janar Tukur Buratai, a ranar Litinin, 4 ga watan Fabrairu ya gana da manyan jami’an rundunar soji a hedkwatar rundunar da ke Asokoro, Abuja.

Jaridar Daily Sun ta ruwaito cewa dukkanin Janar da ke rundunar sun hallara, harda kwamandoji, manyan jami’a da sauransu.

Legit.ng ta tattaro cewa anyi ganawar ne domin sake duba nasarori da kayen da rundunar ta samu a ayyuka daban-daban a fadin kasar.

Zabe: Buratai ya gana da GOCs, kwamandoji da manyan sojoji

Zabe: Buratai ya gana da GOCs, kwamandoji da manyan sojoji
Source: Depositphotos

Akwai kuma hasashen cewa za a tattauna irin rawar ganin da ake sanya ran sojoji za su taka a zabe mai zuwa.

A halin da ake ciki mun ji cewa, Tsofin janar a rundunar soji ta sama, kasa, da ruwa sun bayyana goyon bayan su ga takarar shugaba Buhari domin sake zama shugaban kasar Najeriya a karo na biyu.

KU KARANTA KUMA: Babu wanda zai iya ja da Buhari a zaben 2019 – El-Rufa'i

A yau, Litinin, ne tsofin janar din sojin su ka shaida wa duniya goyon bayan su ga takarar shugaba Buhari a zaben da za a yi ranar 16 ga watan Fabarairu da mu ke ciki.

Tsofin janar-janar din sun hada da ma su mukamin manjo janar 13, Air Vice Marshal (AVM) 8, Rear Admiral 2, birgediya janar 12, Air Commodore 9, Commodore 8 da kuma wasu tsofin shugabannin rundunar soji 17.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel