Kungiyar SERAP ta kai Fashola gaban shari’a saboda kwangilolin wutan lantarki

Kungiyar SERAP ta kai Fashola gaban shari’a saboda kwangilolin wutan lantarki

Mun ji labari kungiyar SERAP ta shiga kotu da Ministan ayyuka da gidaje da kuma wutan lantarki na Najeriya, Babatunde Raji Fashola, tana mai neman a bayyana sunayen kamfanonin da ake ba kwangiloli.

Kungiyar SERAP ta kai Fashola gaban shari’a saboda kwangilolin wutan lantarki

Ana neman tursasawa Fashola ya fitar da sunan wadanda aka ba kwangila
Source: Depositphotos

SERAP tana neman babban kotun tarayya da ke Ikeja a cikin Jihar Legas ta tursasawa Minista Babatunde Fashola ya fito da sunayen manyan kamfanonin da ma’aikatar sa ta ba kwangila tun daga 1999 zuwa yanzu a cikin kasar.

Kungiyar ta SERAP a karar da ta kai gaban Alkalin kotun tarayya mai lamba na FHC/L/CS/105/19, tayi amfani da dokar FOI inda ta nemi Ministan kasar ya fitar da jeringiyar kwangilolin da aka bada na wuta da tituna a cikin Najeriya.

KU KARANTA: Gawurtattun Mayun sun gano cewa Atiku zai doke Buhari a zaben 2019

Kamar yadda mu ka ji, tun a farkon shekarar nan ne kungiyar ta SERAP mai zaman kan-ta, tana nemin jin diddikin duk ayyukan wutan lantarkin da aka bada daga lokacin Obasanjo zuwa yanzu da kuma adadin duk kudin da aka batar.

Bamisope Adeyanju, wanda shi ne babban mai ba kungiyar SERAP shawara kan harkokin shari’a ya fitar da jawabi, yana mai so a bayyanawa Duniya sunayen wadanda aka ba kwangilar wuta domin su san inda kudin gwamnati su ka tafi.

Ana zargin cewa gwamnatin PDP ta kashe makudan kudin da su ka haura dala biliyan 16 wajen gyara wutar lantarki. Sai dai har yanzu ana kukan cewa ba a ga tasirin wannan makudan kudi da aka batar ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel