Mayu sun tsayar da Atiku bayan tattaunawa da dama a tsaunin Obudu da Zuma

Mayu sun tsayar da Atiku bayan tattaunawa da dama a tsaunin Obudu da Zuma

- Kungiyar mayu ta marawa Atiku Abubakar baya a matsayin zabinsu a zaben 2019 mai zuwa

- Sun nuna goyon bayansu ga dan takarar Shugaban kasa na PDP bayan tattaunawa daban-daban wanda suka yi ikirarin sunyi a dutsen Obudu da na Zuma

- Kakakin kungiyar Iboi Okhue ya kuma bayyana cewa nasarar Atiku zai fito musamman daga wata yanki na arewa da ba a yi tsammani ba

A daidai lokacin da yan siyasa ke neman tabbaraki daga yan Najeriya da dama, wata kungiyar mayu ta marawa Atiku Abubakar dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) baya a matsayin zabinsu a zaben 2019 mai zuwa.

Wannan kungiyar mai suna Association of White Witches in Nigeria (AWWN) sun nuna goyon bayansu ga dan takarar Shugaban kasa na PDP bayan tattaunawa daban-daban wanda suka yi ikirarin sunyi a dutsen Obudu da na Zuma.

Mayu sun tsayar da Atiku bayan tattaunawa da dama a tsaunin Obudu da Zuma

Mayu sun tsayar da Atiku bayan tattaunawa da dama a tsaunin Obudu da Zuma
Source: UGC

A cewarsu sun yi amanna da Atiku mai shekara 72 ne zai lashe zaben. Dr. Iboi Okhue, kakakin kungiyar ya sanar da hakan ga jaridar Sunday Independent a hira ta wayar tarho.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama kasurgumin mai garkuwa da mutane a Katsina

Hakazalika, da yake hasashe, Iboi Okhue ya kuma bayyana cewa nasarar Atiku zai fito musamman daga wata yanki na arewa da ba a yi tsammani ba inda abokin amayarsa Muhammadu Buhari na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya kamata ya samu fifiko.

Domin marawa wannan hasashen baya, kakakin kungiyar ya ambaci jihohin da ke yankin arewa, musamman arewa maso yamma, za su yi zaben Atiku sosai a matsayin dn takararsu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel