Buhari ya fadi rukunin 'yan Najeriya da ke goyon bayan sa a yaki da cin hanci

Buhari ya fadi rukunin 'yan Najeriya da ke goyon bayan sa a yaki da cin hanci

A yau, Litinin, ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce talakawan Najeriya na jin dadin yadda gwamnatin sa ke yaki da cin hanci tare da bayyana cewar hakan ne ma ya sa su goyon bayan sa a bangaren ganin an yaki rashawa da cin hanci a kasar nan.

Kazalika, ya ce ma su adawa da shi a kan yana yaki da cin hanci ba su san mene ne cin hanci ba.

Shugaba Buhari na wadannan kalamai ne yayin rantsar da sabbin mambobin kwamitin gudanarwa na hukumar yaki da cin hanci (ICPC) wanda aka yi a fadar shugaban kasa (Villa).

A cewar sa, "wannan taro na yau na daga cikin cigaba da yaki da cin hanci da gwamnati na ke yi a kasar nan. Yaki da cin hanci na daga cikin manyan alkawura uku da na dauka kafin na hau mulki kuma har yanzu da nake takara a karo na biyu ina nan a kan kudirina na cigaba da yaki da cin hanci.

Buhari ya fadi rukunin 'yan Najeriya da ke goyon bayan sa a yaki da cin hanci

Buhari
Source: UGC

"Yaki da cin hanci na da matukar muhimmanci ta fuskar samun cigaba a kasar mu. Hakan ne ya sa nake yawan fadin cewar 'matukar ba mu kashe cin hanci ba, cin hanci zai kashe Najeriya.

"Duk zamu iya zama shaida a kan irin barnar da cin hanci ya yi ga cigaban kasar mu. Cin hanci ne babbar matsalar da ta hana mu motsa wa domin samun cigaba a kasar mu, kuma shine ya jawo zubewar kima da mutuncin kasar mu.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa tsofin janar na soji ba sa tare da Buhari - Oshiomhole

"Cin hanci ya shiga cikin siyasar mu, tattalin arziki da zamantakewar mu. Ma su adawa da yakin da mu ke yi da cin hanci basu san illolin sa ba ne.

"Amma talakan Najeriya ya san mene ne cin hanci kuma ya san illolin sa. Hakan ne ma ya sa su ke goyon kokarin da mu ke yi wajen yaki da cin hanci da rashawa," a kalaman Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel