Babu wanda zai iya ja da Buhari a zaben 2019 – El-Rufa'i

Babu wanda zai iya ja da Buhari a zaben 2019 – El-Rufa'i

- Gwamna Nasir El-Rufa'i ya yi ikirarin cewa ba a taba dan siyasa ko ma'aikacin gwamnati da talakawa suka aminta dashi kamar Buhari ba

- El-Rufai yace babu wanda zai iya ja da Buhari a zaben 2019

- Gwamnan Kadunan yace har yanzu akwai abubuwan da ya kamata a kara gyarawa a gwamnatin Buhari

Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa ba a taba dan siyasa ko ma'aikacin gwamnati da talakawa suka yarda da shi a kasar nan kamar Shugaba Muhammadu Buhari ba.

Gwamnan ya ce 'yan kasar sun san cewa ko a tarihi shugaban kasar bai taba cin amana a mukamai da ayyukan da ya gudanar ba a baya.

El-Rufai wanda ya jadadda hakan a wata hira da manema labarai ya bayyana cewa babu wani dan siyasa da zai iya kayar da dan takarar shugabancin kasar na jam’iyyar APC.

Babu wanda zai iya ja da Buhari a zaben 2019 – El-Rufai

Babu wanda zai iya ja da Buhari a zaben 2019 – El-Rufai
Source: Depositphotos

Ya kuma soki tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo, inda ya ce "idan aka ji Obasanjo na maganganu akwai abin da ya nema a gwamnati bai samu ba. Saboda haka ba don Allah yake yi ba.”

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama kasurgumin mai garkuwa da mutane a Katsina

Sai dai ya bayyana cewa har yanzu akwai abubuwan da ya kamata a kara gyarawa a gwamnatin Buhari.

Amma ba zai bayyana su ba, saboda a cewarsa ba ya ba da shawara a kafafen yada labarai. Ya ce idan zai ba shugaban shawara zai kebe ne da shi a fadarsa.

A baya mun ji cewa Buba Galadima, kakakin kungiyar kamfen din dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya bayyana cewa dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar zai lallasa Shugaban kasa Buhari da kaso 60 zuwa 40 a arewa.

Galadima ya bayyana cewa Atiku zai yi raba daidan kuri’u da Buhari harma a mahaifar Shugaban kasa, wato jihar Katsina.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel