N200,000 na sayar da jariri na domin na kama sana'a - Wata Uwa ta gurfana gaban kotu

N200,000 na sayar da jariri na domin na kama sana'a - Wata Uwa ta gurfana gaban kotu

Da sanadin kafar watsa labarai ta Wuzup Naija mun samu cewa, jami'an tsaro na hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Neja, sun cukwikwiye kugun wasu mutane biyu ababen zargi na aikata laifin fataucin bil Adama.

Ababen zargin biyu, Blessing Aluna mai shekaru 23 a duniya, tare da wani Matashi, Oludare Jeprince mai shekaru 36, sun shiga hannun jami'an tsaro a yankin Madalla dake garin Suleja yayin da suka sace wata karamar yarinya mai shekaru uku kacal a duniya.

Binciken jami'an tsaro ya tabbatar da cewa, Aluna mazauniyar garin Suleja a wani sa'ili daban da ya gabata, ta sayar da jaririn ta 'dan mako guda da haihuwa akan Naira dubu dari biyu yayin da idanun ta suka rufe wajen neman duniya.

Blessing Aluna tare da saurayin ta; Oludare Jeprince

Blessing Aluna tare da saurayin ta; Oludare Jeprince
Source: UGC

Jaridar Northern City ta ruwaito cewa, Aluna tare da taimakon wannan matashi da ya kasance saurayin ta sun ci kasuwar jaririn ta bayan haife shi da mako guda tun a shekarar 2017 da ta gabata.

Yayin nutsawa cikin bincike, Aluna ta yi ruwa da tsaki wajen dillancin sayar da jaririn wata Mata Precious Ade cikin yankin Gwagwalada da ke garin Abuja akan Naira dubu dari biyu da hamsin bayan haife shi da watanni goma sha biyar.

KARANTA KUMA: 2019: Atiku ya samu goyon bayan masarautar Delta

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Aluna ta samu la'adar Naira dubu hamsin da ya kasance ladan wannan mummunan kwazo da aikata wajen yiwa kasa fasadi ta hanyar cin kasuwar ta da fataucin Bil Adama.

Sai dai cikin jawaban ta na rashin tawakkali yayin da jami'an tsaro ke titsiye ta, Aluna ta alakanta fatara gami da talauci da wannan miyagun laifi da ta saba aikatawa domin neman duniya ta kowane hali.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel