Yanzu-yanzu: Kotu ta baiwa INEC umurnin sanya sunayen yan takaran APC na jihar RIbas

Yanzu-yanzu: Kotu ta baiwa INEC umurnin sanya sunayen yan takaran APC na jihar RIbas

Kotun daukaka kara dake birnin Fatakwal ta bada umurnin dakatad da aiwatar da hukuncin babban kotun tarayya da ta bayar na watsi da zabubbukan fidda gwani da jam'iyyar All Progressives Congress, shiyar jihar Ribas ta gudanar.

Tun lokacin, kotun ta haramtawa hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC sanya jam'iyyar APC da yan takaranta a takardan kuri'a na jihar RIbas a zaben 2019.

A ranan 7 ga watan Junairu, Jastis Kolawole Omotosho ya yi watsi da dukkan zaben fidda gwani tsakanin bangaren Magnus Abe da Tonye Cole.

KU KARANTA: Jigo a PDP ya yi kira ga mabiyan jam'iyyar su hallaka alkalan zabe

Yanzu haka jihar Zamfara ce ta rage ba tada yan takaran APC a zaben bana yayinda kotuna biyu daban-daban suka bayar da hukunci masu karo da juna da hallacin musharakarsu a zabe.

Jigo a jam'iyyar APC, Sanata Kabiru Marafa ya ce Hukumar Zabe mai zaman kanta tayi biyaya da umurnin babban kotun Abuja inda ta yanke hukuncin cewa jam'iyyar ta APC ba za ta fitar da 'yan takara ba.

Sanatan wanda kuma shine Ciyaman din kwamitin majalisar dattawa a kan albarkatun man fetur ya yi wannan furucin ne yayin hirar da ya yi da menema labarai a babban birnin tarayya, Abuja.

Ya ce INEC ta tsaya a kan bakar ta na haramtawa jam'iyyar APC reshen Zamfara fitar da 'yan takara saboda gaza gudanar da zaben fidda gwani a cikin lokacin da aka kayyade mata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel