Gwamnatin tarayya za ta rushe wasu makarantun gaba da sakandire - Ministan Ilimi

Gwamnatin tarayya za ta rushe wasu makarantun gaba da sakandire - Ministan Ilimi

- A kokarin ta na son kawo gyara da tsaftace bangaren ilimi, gwamnatin tarayya ta ce za ta rushe wasu makarantun gaba da sakandire

- Rusau din zai shafi jami'o'i 66 da kwalejin kimiyya 68 da gwamnati ta gano cewar haramtattu ne

- Tuni gwamnatin tarayya ta bawa hukumar kula da makarantun gaba da sakandire umarnin daukan matakin gaggawa a kan haramtattun jami'o'i da ke fadin kasar nan

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewar za ta rushe haramtattun makarantun gaba da sakandire saboda irin barazanar da su ke yi ga tsarin ilimi a kasar nan.

Tuni gwamnatin tarayya ta bawa hukumar kula da makarantun gaba da sakandire umarnin daukan matakan gaggawa a kan haramtattun jami'o'i, kwalejin kimiyya, da kwalejin horon malamai da ke fadin kasar nan.

Yanzu haka gwamnatin tarayya ta yi nasarar gano haramtattun jami'o'i 66 da kwalejin kimiyya 68 da ke aiki tare da bayar da takardun shaidar kammala karatu ga jama'a.

Gwamnatin tarayya za ta rushe wasu makarantun gaba da sakandire - Ministan Ilimi

Malam Adamu Adamu; Ministan Ilimi
Source: Facebook

Ministan ilimi, Malam Adamu Adamu, ne ya sanar da hakan yayin hutun karshen mako a Abuja, birnin tarayya.

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta kama 'yan dabar siyasa da muggan makamai, hotuna

Ministan ya ce an samu raguwar makarantun na bogi bayan umarnin daukan mataki a kan su da gwamnati ta bayar.

Kazalika ya yi kira ga jama'a da su taimaka wajen bayar da bayanai a kan irin wadannan makarantu na bogi domin a dauki matakin da ya dace a kan lokaci.

"Ba zamu ji nauyin rushe irin wadannan haramtattun makarantu ba," a cewar Malam Adamu Adamu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel