Danki: Rikici ya barke tsakanin lauyan Onnoghen da shugaban kotun CCT

Danki: Rikici ya barke tsakanin lauyan Onnoghen da shugaban kotun CCT

Wani dan karamin rikici ya barke a zauren kotun hukunta ma'aikatan gwamnati wato CCT a ranan Litinin inda ake gurfanar da tsohon babban alkalin Najeriya, Walter Onnoghen, wanda ake zargi da almundahana.

Shugaban kotun, Danladi Umar, ya tuhumci da lauyan Walter Onnoghen, Adeboyega Awomolo, da kokarin jinkirtar da karar ta hanyar yi musu wasa da hankali.

Awomolo ya bukaci kotun da daga karan zuwa ranan Alhamis saboda sauraron hukuncin da majalisar kolin shari'a NJC zata yanke kan al'amarin saboda kada a samu tanakudi. NJC zata zauna ranan Laraba.

Cikin fushi, sai Awomolo ya tashi tsaye kuma kalubalanci shugaban CCT. Ya ce shekaransa 25 babban lauya kuma shekaran 45 kenan da aikin lauya, saboda haka, ba zai lamunci Danladi Umar ya ci mutuncisa gaban kananan lauyoyi ba.

An kwashe mintuna 10 ana sa'insa har sai da aka dakatad da zaman domin baiwa lauyoyin daman yarjejeniya tsakaninsu.

KU KARANTA: Dubun wasu gagararrun yan fashi ta cika yayin da suka yi arba da Yansanda

An koma kotun ladabtar da ma'aikatan gwamnati wato CCT da safen nan domin cigaba da gurfanar da sallamammen shugaban Alkalan Najeriya, Jastis Walter Onnoghen, a birnin tarayya Abuja.

An koma kotun a ranan Litinin ne sakamakon watsi da karar Onnoghen da kotun daukaka kara tayi a ranan Laraban da ya gabata inda ya bukaci kotun ta hana CCT gurfanar da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel