Ba mu gabatar da kowani doka da ya aminta da kafa jami’ar Musulunci ba – Majalisar dokokin jihar Imo

Ba mu gabatar da kowani doka da ya aminta da kafa jami’ar Musulunci ba – Majalisar dokokin jihar Imo

- Majalisar dokokin jihar Imo ta karyata shirin samar da wata doka da zai bayar da damar kafa wata jami’ar Musulunci a jihar

- Majalisar na fuskantar suka biyo bayan zargin cewa tana shirin mara wa wani doka baya da zai bayar da damar kafa jami’ar Musulunci a jihar

- Yan majalisaar sun bayyana cewa sun kawai dokar da suka kafa shine na samar da makarantun koyon ilimin jinya da karban haihuwa

Rahotanni sun kawo cewa majalisar dokokin jihar Imo ta karyata shirin samar da wata doka da zai bayar da damar kafa wata jami’ar Musulunci a jihar.

Sakataren labarai na kakakin majalisar dokokin jihar Imo, Marcel Ekwezuo, ya bayyana hakan a Owerri, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ba mu gabatar da kowani doka da ya aminta da kafa jami’ar Musulunci ba – Majalisar dokokin jihar Imo

Ba mu gabatar da kowani doka da ya aminta da kafa jami’ar Musulunci ba – Majalisar dokokin jihar Imo
Source: UGC

Majalisar dokokin jihar Imo na fuskantar suka biyo bayan zargin cewa tana shirin mara wa wani doka baya da zai bayar da damar kafa jami’ar Musulunci a jihar.

Amma majalisar dokokin jihar tace bata gabatar da kowani doka akan samar da jami’ar Musulunci ba.

KU KARANTA KUMA: Tashin hankali yayinda rikici ya kaure a tsakanin magoya bayan APC da PDP a Delta

Yan majalisaar sun bayyana cewa sun kawai dokar da suka kafa shine na samar da makarantun koyon ilimin jinya da karban haihuwa mallakar kungiyoyin addinai da sauran kungiyoyi masu zaman kansu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel