Babbar kotu ta tsayar da shari’an Fayose tsawon sa’a guda

Babbar kotu ta tsayar da shari’an Fayose tsawon sa’a guda

- Babbar kotun tarayya da ke jihar Lagas ta tsayar da shari’an tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Peter Fayose na tsawo sa’a guda

- Jim kadan bayan an fara zaman kotu sai Justis Mojisola Olatoregun da ke rike da shari’an, ta tashi domin halartan wani aiki

Wata babbar kotun tarayya da ke jihar Lagas a ranar Litinin, 4 ga watan Fabrairu ta tsayar da shari’an tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Peter Fayose na tsawo sa’a guda.

Tsohon karamin ministan tsaro, Saanata Musiliu Obanikoro, wanda ya kasance shaida na biyar a shari’an, ya halarci wani gwani a ranar Litinin, NAN ta ruwaito.

Babbar kotu ta tsayar da shari’an Fayose tsawon sa’a guda

Babbar kotu ta tsayar da shari’an Fayose tsawon sa’a guda
Source: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa a zaman karshe da aka yi, a ranar 21 ga watan Janairu, ya tabbatar da cewa Fayose ya karbi dala miliyan biyar da wasu adadin kudade na naira daga asusun tsohon mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki (mai ritaya) a watan Yunin 2014.

KU KARANTA KUMA: EFCC ta yanke wa masu laifi 40 hukunci cikin wata daya kacal

Justis Mojisola Olatoregun da ke rike da shari’an, ta tashi jim kadan bayan an fara zaman kotu domin halartan wani aiki. Tace za ta dawo nan da dan sa’a guda domin a ci gaba da shari’an.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gurfanar da Fayose a ranar 22 ga watan Oktoba 2018 tare da wani kamfani, Spotless Investment Ltd., kan tuhume-tuhume 11.

Sai dai ya ki amsa laifin, sannan aka bayar da belinsa kan kudi naira miliyan 50.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel