Tashin hankali yayinda rikici ya kaure a tsakanin magoya bayan APC da PDP a Delta

Tashin hankali yayinda rikici ya kaure a tsakanin magoya bayan APC da PDP a Delta

- Rahotanni sun kawo cewa mutun daya ya mutu yayinda rikici ya kaure a tsakanin magoya bayan APC da PDP a Delta

- Lamarin ya afku a Effurun, karamar hukumar Uvwie ranar Lahadi, 3 ga watan Janairu

- Zaman lafiya ya dawo yakin bayan da sojoji daga wani bataliya da ke kusa da Effurun suka shiga lamarin

An samu rudani a Effurun, karamar hukumar Uvwie da ke jihar Delta lokacin da wasu magoya bayan jam’iyyun siyasa biyu ta APC da PDP suka kara a ranar Lahadi, 3 ga watan Fabrairu.

Jaridar Daily Sun ta ruwaito cewa mutun daya ya mutu sannan wasu da dama suka samu rauni a lokaci faruwar lamarin.

Legit.ng ta tattaro cewa an rufe shaguna da wuraren bauta a yankin, yayinda mazauna yanki da dama ke tsoron komawa yankin.

Tashin hankali yayinda rikici ya kaure a tsakanin magoya bayan APC da PDP a Delta

Tashin hankali yayinda rikici ya kaure a tsakanin magoya bayan APC da PDP a Delta
Source: Depositphotos

An rahoto cewa zai da sojoji daga wani bataliya da ke kusa da Effurun suka shiga lamarin kafin samu rikicin ya lafa sannan zaman lafiya ya dawo yankin.

A baya mun ji cewa 'yan ta'adda sun farwa mambobin jam'iyyar APC a yayin da suke gudanar da gangamin yakin zabensu a garin Sagbama da ke jihar Bayelsa, harin dai ya jawo asarar ran mutum daya da jikkata mutane biyu.

KU KARANTA KUMA: EFCC ta yanke wa masu laifi 40 hukunci cikin wata daya kacal

Wani mazaunin garin Sagbama wanda harin ya faru akan idanunsa ya ce akalla 'yan ta'addan sun kai 15, inda suka yi amfani da muggan makamai wajen tarwatsa jama'ar da ke a filin yakin zaben.

Kawo agajin gaggawa da rundunar 'yan sanda ta yi a wajen ya hana lamarin kara munana, a cewar mazaunin garin.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel