Yanzu-yanzu: An koma kotu da safen nan, Walter Onnoghen ya sake kunnen jaki

Yanzu-yanzu: An koma kotu da safen nan, Walter Onnoghen ya sake kunnen jaki

An koma kotun ladabtar da ma'aikatan gwamnati wato CCT da safen nan domin cigaba da gurfanar da sallamammen shugaban Alkalan Najeriya, Jastis Walter Onnoghen, a birnin tarayya Abuja.

An koma kotun a ranan Litinin ne sakamakon watsi da karar Onnoghen da kotun daukaka kara tayi a ranan Laraban da ya gabata inda ya bukaci kotun ta hana CCT gurfanar da shi.

Har ila yau, Walter Onnoghen ya ki bayyana kansa a kotun CCT duk da umurnin da akayi Masa, Alkalin kotun, Jastis Danladi Umar, ya jaddada cewa wajibi ne tsohon Alkalin alkalan ya zo kotu da kansa.

Saboda haka, an daga gurfanar zuwa ranan 11 ga watan Febrairu, 2019.

KU KARANTA: Dubun wasu gagararrun yan fashi ta cika yayin da suka yi arba da Yansanda

Mun kawo muku rahoton cewa kotun daukaka kara ta yi watsi da karar da korarren shugaban alkalan Najeriya, Jastis Walter Onnoghen, ya shigar domin tsagaita gurfanarsa a kotun hukunta ma'aikatan gwamnati wato CCT.

Alkalin kotun daukaka karan, Jastis Abdul Aboki, ya yi watsi da karan ne saboda sashe na 306 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya haramta tsagaita gurfanar wani mutum idan ya aikata babban laifi.

Kotun a ranan Laraba tace bukatar da Onnoghen ya kawo kwanko ne saboda babu wani dalili a shari'a da zai amsa irin wannan bukata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel