2019: Atiku ya samu goyon bayan masarautar Delta

2019: Atiku ya samu goyon bayan masarautar Delta

- Yayin da zaben shugaban kasa ya gabato Atiku ya samu goyon bayan masarautar jihar Delta

- Masarautar Delta ta nemi talakawan ta da su tabbatar da nasarar Atiku a yayin babban zabe

- Mai martaba Sarkin Delta, Efeizomor Emmanuel, ya ce Atiku ya cancanci goyon baya kasancewar abokin takarar sa haifaffan 'da ne a kasar Ibo

Mun samu cewa, a yayin da babban zaben kasa ya ke daf da gudana, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya samu kwarin gwiwa ta cimma nasara yayin da wata babbar masarauta ta goya masa baya.

Masarautar jihar Delta ta bayyana sanarwar goyon bayan ta ga dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar da kuma abokin takarar sa, Peter Obi da ya kasance tsohon gwamnan jihar Anambra.

Atiku yayin taron sa na yakin neman zabe a jihar Delta

Atiku yayin taron sa na yakin neman zabe a jihar Delta
Source: Twitter

Babban jagora na masarautar, Sarkin fadar Owa, mai martaba Obi Efiezomor Emmananuel, shine ya bayar da shaidar hakan yayin gudanar da taron yakin neman zabe na ja'm'iyyar PDP cikin garin Delta a karshen makon da ya gabata.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, Sarki Emmanuel ya bayyana abokin takarar Atiku a matsayin haifaffan 'da na kasar Ibo kasancewar makotaka dake tsakanin jihar Delta da kuma Anambra.

Ya ke cewa, dole ne a ramawa Kura kyakkyawar aniyarta domin kuwa Peter Obi ya yiwa jihar Delta gagaruma da sauke nauyin makotaka bisa ga tanadi na jagoranci yayin da ya ke rike da kujerar gwamnatin jihar Anambra.

KARANTA KUMA: Sauyin yanayi ya haddasa kifewar jirgin mataimakin shugaban kasa

Basaraken ya yi kira ga al'ummar jihar Delta da su fito kwansu da kwarkwata wajen jefa kuri'un sa ga Atiku yayin babban zaben kujerar shugaban kasa da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu.

Kazalika shafin jaridar Legit.ng ya ruwaito cewa, Atiku ya zubar da hawayen murna yayin da ya samu goyon bayan kungiyar dattawan Arewa, Kudu da kuma kungiyar dattawan yankin Neja Delta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel