Hukumar INEC ta dauki alwashin baiwa yan siyasa mamaki a zaben 2019

Hukumar INEC ta dauki alwashin baiwa yan siyasa mamaki a zaben 2019

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta bayyana cewa ta samar da wasu tsare tsare da zasu dakile mummunan halayyar nan ta yan siyasa na sayen kuri’u a yayin zabe, a babban zaben shekarar 2019, inji rahoton jaridar Premium Times.

Kwamishinan hukumar INEC, Festus Keyamo ne ya sanar da haka a yayin da yake zantawa da manema labaru a babban birnin tarayya Abuja, a ranar Lahadi, 3 ga watan Feburairu, inda yace hukumar ta kirkiro wasu matakan hana sayen kuri’u.

KU KARANTA: Mi’ara koma baya: Kungiyar dattawan Najeriya ta musanta goyon bayan Atiku

Matsalar sayen kuri’u ta yawaita a zabukan gwamnoni da aka yi a kwanakin baya, musamman a jihohin Anambra, Ondo, Ekiti, Edo da Osun, inda aka kama yan siyasa da dama suna sayen kuri’un masu kada kuri’a, ko kuma su basu kayan abinci.

Mista Festus yace ba zasu bayyana matakan da suka kirkira don yaki da cinikin kuri’u ba, saboda a cewarsa hukumar ta fahimci cewar yan siyasa na kirkiran sabbin hanyoyin sayen kuri’un jama’a, don haka ba zasu fallasa matakan ba.

A wani labarin kuma, kwamishinan INEC, Festus ya bayyana cewa hukumar ba za tayi amfani da na’urar kwamfuta wajen tattara sakamakon zaben shekarar 2019 ba, inda yace hukumar za ta yi amfani da hannu ne wajen tattara kuri’un ne.

Da cewar Festus; “Muna sane da kudurin dokar dake gaban majalisa da zata bada daman tattara kuri’u ta hanyar na’ura mai kwakwalwa, tattara sakamakon zabe ta na’ura mai kwakwalwa nada muhimmanci, don haka zamu jira mu ga yadda zata kaya a majalisar.’

Daga karshe kwamishinan zaben yace jam’iyyu Casa’in da daya, 91, ne zasu fafata a zaben 2019, zaben da ake sa ran mutane miliyan tamanin da hudu da dubu hudu da tamanin da hudu, 84,004,084 zasu kada kuri’a a cikinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel