Mi’ara koma baya: Kungiyar dattawan Najeriya ta musanta goyon bayan Atiku

Mi’ara koma baya: Kungiyar dattawan Najeriya ta musanta goyon bayan Atiku

Kungiyar dattawan jihohin Arewa ta tsakiya, ta janye goyon bayan da ta baiwa dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, inda tace rahotannin da ake watsawa game da haka ba gaskiya bane tun da fari.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin kungiyar, Godwin Egbunu ne ya bayyana haka a ranar Litinin, 4 ga watan Janairu, inda yace kungiyarsu bata taba ayyana goyon baya ga takarar Atiku Abubakar ba.

KU KARANTA: Gwamnan Zamfara ya sauke sakarakunan gargajiya 11 daga mukamansu

“Cikin bakin ciki na kalla tare da sauraron wani mutumi mai suna Bitrsuk Pogu dake shugabantar kungiyar al’ummar garin Chibok mazauna babban birnin tarayya Abuja yana ikirarin yin magana da yawun kungiyar jihohin Arewa ta tsakiya.

“Babu wani lokaci da muka taba bayyana goyon baya ga takarar Atiku Abubakar a zaben dake karatowa ba, bamu taba goyon bayansa ba, kuma ba zamu goyi bayansa ba, jama’anmu suna yi ma labarin nan kallon labarin kanzon kurege.

“Don haka muke kira ga jama’a dasu yi watsi da wannan labari, idan har da akwai bukatar bayyana goyon baya ga wani dan takara, zamu sanar jama’a a lokacin daya dace, saboda jama’an Arewa ta tsakiya mutane ne masu akida da ba zasu sayar da yancinsu ba.” Inji shi.

A ranar Lahadi ne wasu kungiyoyi suka tabbatar da goyon bayansu ga takarar Atiku Abubakar, inda suka ce Atiku ne yafi dacewa da Najeriya domin ya fidda A’I daga rogo, kungiyoyin sun hada da kungiyar Yarbawa Afenifere, ta Inyanmurai Ohanaeze Ndigbo, PANDEF, da kungiyar jihohin Arewa ta tsakiya.

Sai dai kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi watsi da kungiyoyin, inda ta bayyana kungiyoyin a matsayin marasa tasiri a siyasar Najeriya, don haka ba zasu iya kawo ma nasarar Buhari cikas a zaben 2019 ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel