EFCC ta yanke wa masu laifi 40 hukunci cikin wata daya kacal

EFCC ta yanke wa masu laifi 40 hukunci cikin wata daya kacal

- Hukumar EFCC ta yi nasarar yanke hukunci 40 a wata daya da ya gabata

- Ofishin Lagas ta kama masu laifi 20, sai ofishin Abuja mai tara

- Shida kuma daga Port Harcourt da Kaduna ne inda kowanne ke da uku

Tonu Orilade, kakakin hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zago kasa (EFCC), yace hukumar ta yankewa masu laifi 40 hukunci a watan Janairu.

Ya bayyana hakan a wani jawabi a ranar Lahadi a Abuja, inda ya kara da cewa adadin mutane ya kasance waadanda aka kama da laifi a fadi ofishoshin hukumar na yankuna daban-daban.

Orilade yace adadin yan nuna cewa ofishin hukumar na Lagas na da mutane 20, sai ofishin Abuja da ke da tara.

EFCC ta yanke wa masu laifi 40 hukunci cikin wata daya kacal

EFCC ta yanke wa masu laifi 40 hukunci cikin wata daya kacal
Source: Facebook

“Shida kuma daga Port Harcourt da Kaduna ne inda kowanne ke da uku. Kano kuma na da biyu, yayinda Benin, Ibadan, Gombe ke da daddaya,” inji shi.

Orilade ya bayyana cewa wadanda aka yankewa hukunci harda tsoffin jami’an hukumar zabe mai zaman kanta su biyu, inda ya kara da cewa an yanke masu shekaru 91 a gidan yari da kuma kwace kadarorinsu inda aka mallaka ta ga gwamnatin tarayya.

Kakakin ya kara da cewa hakazalika an yankewa wani Adewale Dalmeida, wani ma’aikacin Dangote Cement Group shekaru biyar a gidan yari.

KU KARANTA KUMA: Jihar Benue ta shiga alhini sakamakon mutuwar Sanata Waku

Ya bayyana cewa an daure Dalmeida kan laifin karkatar da manyan motoci tara cike da buhuhunan siminti 800 kowanne wanda kudinsu ya kai naira miliyan 15 kowanne wanda mallakar ubangidan nasa.

Orilade ya bayyana cewa sabon manufar hukumar na kamo yan damfara ya haifar da yaya masu idanu biyo bayan sabon hanyar damfara ta intanet.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel