Sauyin yanayi ya haddasa kifewar jirgin mataimakin shugaban kasa

Sauyin yanayi ya haddasa kifewar jirgin mataimakin shugaban kasa

A ranar Asabar ta makon da ya gabata jirgi mai saukar angulu da ya yo jigilar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo tare da tawagar sa ta mutum tara, ya samu tangarda yayin dira inda ya kife a garin Kaaba na jihar Kogi.

A jiya Lahadi, kamfanin jirgin na Caverton ya yi karin haske tare da zayyana abin da ya haddasa kifewar jirgin yayin saukar sa a garin Kaaba, inda ya jingina rashin kyakkyawan sauyin yanayi a matsayin tagardar da jirgin mai saukar angulu ya fuskanta.

Kamfanin Caverton mamallakin jirgin da azal ta afkawa, ya ce a halin yanzu hukumomi masu ruwa da tsaki sun tsunduma cikin bincike gadan-gadan domin tabbatar da sahihanci akan ummul aba isin da ta haddasa kifewar sa.

Kamar yadda majiyar ta jaridar Legit.ng ta ruwaito, hukumar kamfanin ta kuma sake jaddada tsayuwar daka akan inganta harkokin ta na gudanarwa domin tabbatar da matsananciyar nagarta ta jiragen ta.

KARANTA KUMA: Zazzabin Lassa ya salwantar da rayukan Mutane 6, 40 sun kamu a jihar Filato

Ko shakka ba bu an kwashe lafiya yayin da Mataimakin shugaban kasar ya tsira kalau tare da tawagar sa da ko kwarzane ba bu wanda ya samu yayin aukuwar tsautsayin da Hausawa kan ce ba ya wuce ranar sa.

Da yawa daga cikin manyan kasar nan sun jajantawa Farfesa Osinbajo tare da taya sa murna gami da farin ciki dangane da yadda tsautsayin ya auku ba tare da wani akasi ba na samun rauni ko mai gaba daya ta salwantar rai.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel