Gwamnan Zamfara ya sauke sakarakunan gargajiya 11 daga mukamansu

Gwamnan Zamfara ya sauke sakarakunan gargajiya 11 daga mukamansu

Gwamnan jahar Zamfara, Abdul Aziz Yari ya dauki tsatstsauran mataki akan wasu sarakunan gargajiya a jahar Zamfara, ta hanyar saukesu daga mukamansu bayan bayanai sun bayyana cewa suna da hannu cikin hare haren yan bindiga dake faruwa a jahar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin sarakan gargajiyan na baya baya da ake tuhuma akwai Mai Wurno, Alhaji Bello da Alhaji Aliyu Dangaladiman Birnin Magaji, kamar yadda kaakakin rundunar tsaron farin kaya ta civil defence, Aminu Isa Maru ya bayyana.

KU KARANTA: Siyasar Kano: Lokutta 3 da aka kwashi yan kallo tsakanin Shekarau da Kwankwaso

Kaakakin yace tuni hakiman sun bayyana a babban ofishin rundunar dake garin Gusau, inda suka amsa tambayoyi game da hannu cikin karya dokar da gwamnati ta saka na hana sayar da man bumburutu a jahar Zamfara.

Shima kwamishinan kananan hukumomi, Alhaji Bello Dankande Gamji yace gwamnatin jahar ta haramta sayar da mai a galan galan ga yan bindiga, amma sai hakiman suka aika ma shuwagabannin yan bumburutu cewa su cigaba da sayar da mansu babu matsala.

Haka zalika Gwamna Abdul Aziz Yari ya sauke wasu hakimai daga mukamansu sakamakon bankado hannayensu cikin tabarbarewar tsaro a jahar, hakiman sun hada da hakimin Ruwan Gora dake cikin karamar hukumar Talatar Mafara, Alhaji Isa Balarabe.

Hakimin Ruwan Rana Alhaji Altine Magaji, da hakimin Ruwan Jema’a, Alhaji Sani Ruwan Rana, hakimin Baichin Birane Marafa Zubairu, dagacin kauyen Tugar Dutse, Hassan Muhammad, dagacin Gyado Danjekan Gyado, hakimin Ruwan Gora ta karamar hukumar Bukuyyuma Alhaji Ishaq Sadik da hakimin Gwalli Alhaji Musa Gwalli.

Wani daga cikin hakiman da aka tsige wanda lamarinsa ya ta’azzara, shine hakimin Gurbin Bore ta karamar hukumar Zurmi, Alhaji Bello Magaji wanda ake zargi da hada kai da yan bindiga suka sace matar kwamishinan wasannai na jahar Zamfara, Abdullahi Gurbin Bore da yayansa.

Bincike ya nuna yan bindigan sun karbai naira miliyan 10 a matsayin kudin fansa daga kwamishina kafin su sako masa iyalansa, inda daga ciki suka baiwa hakimin naira dubu dari takwas (N800,000) a maimakon naira miliyan daya da suka yi masa alkawari da fari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel