Dubun wasu gagararrun yan fashi ta cika yayin da suka yi arba da Yansanda

Dubun wasu gagararrun yan fashi ta cika yayin da suka yi arba da Yansanda

Rundunar Yansandan jahar Enugu ta sanar da kama wasu gagga gaggan miyagun mutane su biyar da suka shahara wajen fashi da makami tare da satar mutane da nufin yin garkuwa dasu a yayin wani samame da ta kaddamar a mabuyarsu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin Yansandan, SP Ebere Amaraizu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Lahadi, 3 ga watan Feburairu, inda yace Yansanda sun kama barayin ne a ranar Asabar.

KU KARANTA: Siyasar Kano: Lokutta 3 da aka kwashi yan kallo tsakanin Shekarau da Kwankwaso

Ebere ya bayyana cewa Yansandan yankin yammacin Nkanu ne suka samu nasarar kama barayin bayan samun wasu bayanan sirri game da ayyukan miyagun, wanda hakan ya sabbaba Yansanda suka kaddamar da farmaki a mabuyarsu dake yankin Amakatanga cikin karamar hukumar Nkanu.

Kaakaki Ebere ya bayyana sunayen masu garkuwan kamar haka; Nwafor mai shekaru 23, Chukwu Ebuka 28, Nelson Morris 24 da kuma Ikechukwu Onwuabueke, dukkaninsu mazauna jahar Abia, sai kuma wata mace mai suna Miriam Oguejiofor.

Ebere yace yan bindigan sun sace wani mutumi mai suna Anthony Okeke ne bayan Miriam ta gayyaceshi zuwa garin Agbani na jahar Enugu da nufin kulla wata yarjejeniyar kasuwanci, inda isarsa keda wuya zuwa inda suka shirya, sai sauran gungun yan bindigan suka fito, suka yi awon gaba da shi.

“Da farko dai yan bindigan sun nemi a biyasu kudin fansa naira miliyan 10, amma daga bisani suka rage kudin zuwa naira miliyan 5, kafin daga bisani Yansanda suka mamayesu, suka afka ma mabuyar yan bindigan, suka kamasu, tare da ceto mutumin da suka yi garkuwa da shi.” Inji shi.

Zuwa yanzu, kaakakin rundunar Yansandan ya bayyana cewa miyagun sun basu hadin kai a binciken da suke yi, sa’annan ya yi kira ga sauran jama’an yankin dasu zamto masu takatsantsan game da tsaro.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel