Jihar Benue ta shiga alhini sakamakon mutuwar Sanata Waku

Jihar Benue ta shiga alhini sakamakon mutuwar Sanata Waku

Allah ya yi wa Sanata Joseph Kennedy Waku rasuwa yana da shekara 73 a duniya, jadridar THISDAY ta ruwaito.

A cewar rahoton, Sanata Waku yrasu a ranar Lahadi, 3 ga watan Fabrairu a asibitin National Hospital da ke Abuja bayan yar gajeruwar rashin lafiya.

An haifi Sanata Waku a ranar 12 ga watan Yuni, sannan an zabe shi a matsayin sanata mai wakiltan Benue ta arewa maso yamma a majalisar dokokin kasar a 1999 karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Jihar Benue ta shiga alhini sakamakon mutuwar Sanata Waku

Jihar Benue ta shiga alhini sakamakon mutuwar Sanata Waku
Source: Twitter

Sanata Waku wanda ya kasance dan kauyen Waku a karamar hukumar Guma na jihar Benue y kasance a majalisar dattawa tsakanin 1999 da 2003.

Har zuwa mutuwarsa, Waku ya kasance igo a kungiyar siyasar arewa ta Arewa Consultative Forum.

Ya kasance daya daga cikin masu fada a ji a Benue wanda ke Allah wadai da hare-haren makiyaya a jihar.

Za a fi tuna Waku da babban adawa da yake yi ga gwamnatin tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo yayinda yake a matsayin sanata.

KU KARANTA KUMA: Dubun wasu gagararrun yan fashi ta cika yayin da suka yi arba da Yansanda

A baya mun ji cewa Babafemi Ojudu, wani hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fuskar harkokin siyasa, a ranar Lahadi ya godewa jami'an kai agajin gaggawa da suka kai masu daukin ceto a lokacin da jirgi mai saukar angulu da suke ciki ya yi hatsari tare da faduwa a ranar Asabar.

Mr Ojudu yana daya daga cikin tawagar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinba a lokacin da lamarin ya afku, a lokacin da jirgin ke kokarin sauka a garin Kabba, jihar Kogi.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa jirgin ya fadi ne da misalin karfe 3:00 na rana, inda Osinbajo da Ojudu suka tsira da rayukansu ba tare da ko kwarzane ba, tare da wasu mutane 10 da ke cikin jirgin.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel