Ma’aikatan Kananan Hukumomi za su goyawa Okowa baya a Jihar Delta

Ma’aikatan Kananan Hukumomi za su goyawa Okowa baya a Jihar Delta

- Ifeanyi Okowa na jihar Delta yayi kira ga mutane game da zaben 2019

- Gwamnan na Delta ya nemi mutane su zabi wadanda za su iya yin aiki

- A makon jiya ne kungiyar NULGE ta yi wa gwamnan na PDP mubaya’a

Ma’aikatan Kananan Hukumomi za su goyawa Okowa baya a Jihar Delta

Gwamna Okowa yace a zabi wadanda za su iya yin aiki
Source: Twitter

Mun ji cewa Gwamnan jihar Delta, mai girma Ifeanyi Okowa yayi kira ga mutanen jihar sa da su zabi ‘yan siyasar da za su tabuka masu abin kirki a zaben bana na 2019. Gwamnan yayi wannan kira ne a Ranar Asabar dinnan.

Ifeanyi Okowa ya fadawa jama’a su fito su marawa ‘yan takarar da su ka dace baya a zaben da za ayi. Okowa yace idan aka zabi ‘yan takarar da su ka san aiki ne za a ga cigaba a jihar Delta da ma kuma fadin Najeriya gaba daya.

KU KARANTA: ‘Dan takarar Jam’iyyar adawa yayi wa Buhari alkawarin miliyoyin kuri’u a Kano

Kamar yadda mu ka samu labari, hakan na zuwa ne bayan kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi na NULGE ta yi wa gwamnan mubaya’a a zaben na bana. Gwamna Okowa ya ji dadin wannan kwaurin gwiwa da ya samu.

Gwamna Ifeanye Okowa ya nemi kungiyar ta NULGE ta kuma ja hankalin ‘ya ‘yan ta su mara masa baya domin ya zarce tare da kuma sauran ‘yan takarar PDP. Gwamnan na PDP yace ya na sa rai cewa zai koma kan kujerar sa.

Okowa wanda yake neman karasa wa’adin sa bayyanawa mutanen sa cewa su kwantar da hankalin su domin babu wanda ya isa ya murde zaben bana. Ma’aikatan jihar sun yaba da yadda gwamna Okorowa yake biyan albashi a kan-kari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel