Gwamnatin Tarayya na kitsa yadda za ta damke wasu Alkalai – Gwamnan Ribas

Gwamnatin Tarayya na kitsa yadda za ta damke wasu Alkalai – Gwamnan Ribas

- Nyesom Wike ya zargi Buhari da neman kama wasu Alkalai

- Gwamnan yace Gwamnatin Tarayya za ta yi wa Alkalan cinne

- Wike yace ya samu wannan labari ne ta wajen wani Minista

Gwamnatin Tarayya na kitsa yadda za ta damke wasu Alkalai – Gwamnan Ribas

Gwamnan Ribas Nyesom Wike yace ya ji ana neman kama wasu Alkalai
Source: Depositphotos

Mun ji labari cewa mai girma gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas yana zargin Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewa tana neman kama wasu manyan Alkalai da ake ji da su a kotun tarayyan kasar nan.

Nyesom Wike yayi wannan bayani ne a jiya Ranar Lahadi 3 ga Watan Fabrairu bayan ya halarci hudubar da aka yi a babban cocin nan na Greater Evangelism World Crusade da ke babban birnin Fatakwal a cikin jihar Ribas.

Gwamnan yace kwanan nan ne gwamnatin APC za ta kama wasu Alkalai fiye da 200 tayi masu sharri, inda yace duk Alkalin da yayi gardama zai gamu da fushin gwamnatin tarayya inda za a tasa sa gaba a hana sa sakat.

KU KARANTA: Dalilin da ya sa tsofaffin Sojojin Kasar nan ba sa tare da Buhari - Oshiomhole

Mista Wike yayi kira ga Kiristocin jihar sa da su dukafa da yi wa Alkalan Najeriya addu’a inda yace ana neman ganin bayan su. Gwamnan na PDP yace taba Alkalai babban hari ne a kan damukaradiyyar Najeriya gaba daya.

Mai girma gwamnan dai yace daga cikin Alkalan za a taba akwai masu aiki a kotun koli da kuma Alkalab kotun daukaka kara da manyan Alkalan kotun tarayya. Gwamnan yace ya ji wannan labari ne wajen wani Minista.

Gwamnan na Ribas ya taba yin irin wannan ikirari a kwanakin baya inda yace za a toshe kafofin yanar gizo a lokacin zaben 2019. Tuni dai gwamnatin kasar ta musanya wannan batu ta bakin ofishin NSA.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel