Babu maganar tsige Gwamnan Jihar Legas yanzu – Tinubu ya sa baki

Babu maganar tsige Gwamnan Jihar Legas yanzu – Tinubu ya sa baki

Mun ji cewa babban jigon jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana cewa babu maganar tsige gwamnan Legas Mista Akinwunmi Ambode daga kan kujerar sa a halin yanzu.

Babu maganar tsige Gwamnan Jihar Legas yanzu – Tinubu ya sa baki

Bola Tinubu ya sa baki a cikin rikicin Gwamnan Jihar Legas da 'Yan Majalisa
Source: Twitter

Bola Tinubu yayi wannan jawabi ne bayan zaman da aka yi domin sulhu tsakanin manyan jam’iyyar APC mai mulki da kuma majalisar dokokin jihar Legas. A baya ‘yan majalisar jihar sun yi barazanar tsige gwamna Ambode.

Asiwaju Tinubu yake cewa ‘yan majalisar jiha za su hada-kai da gwamnan jihar su yi aiki tare da juna domin jihar Legas ta tsira. Tinubu yace sun yi bincike game da silar rikicin da ya barko, sun kuma shawo kan duk matsalolin.

KU KARANTA: Mutum 2 sun mutu yayin da da yawa su ka raunata wajen kamfen din APC

Tsohon gwamna Bola Tinubu ya na mai cewa a siyasa a kan samu rikici irin wannan, sai dai yace a matsayin su na gida guda, an yi sulhu tsakanin majalisa da kuma Mista Akinwumi Ambode wanda ba zai nemi takara wannan karo ba.

An yi wannan taro na sulhu ne a Lagos House da ke Marina inda mataimakiyar gwamna Ambode watau Idiat Adebule da kuma kakakin majalisar dokokin jihar Legas da mataimakin sa; Mudashiru Obasa; Wasiu Eshinlokun su ka halarta.

Sauran wadanda aka yi zaman da su sun hada da manyan majalisar jihar irin su Sinai Agunbiade; da Rotimi Abiru, da kuma kusoshin jam’iyyar APC, sai ‘Dan takarar APC, Babajide Sanwo-Olu da Mataimakin sa Dr Femi Hamzat.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel