Magoya baya na za su zabi Shugaban kasa Buhari – ‘Dan takarar GPN, Zaura

Magoya baya na za su zabi Shugaban kasa Buhari – ‘Dan takarar GPN, Zaura

Mun ji labari cewa ‘dan takarar gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar nan ta Green Party of Nigeria, GPN watau Abdussalam Zaura, ya sha alwashin tarawa shugaban kasa Muhammadu Buhari tarin kuri’u.

Magoya baya na za su zabi Shugaban kasa Buhari – ‘Dan takarar GPN, Zaura

Mutanen AA Zaura za su yi Shugaban kasa Buhari a zaben 2019
Source: UGC

Mai neman kujerar gwamnan jihar Kano a zaben na 2019 ya bayyana cewa zai tarawa shugaba Buhari na APC kuri’u akalla miliyan 2. Alhaji Zaura ya bayyana cewa zai goyi bayan Buhari ne a zaben shugaban kasa na bana.

AA Zaura ya nuna cewa yana tare da shugaba Buhari ne saboda tun can yana cikin masu kaunar sa kuma yana kallon sa a matsayin abin koyin sa. AA Zaura yayi wannan bayani ne wajen wani taro da yayi da ‘yan jarida a Kano.

KU KARANTA: Yadda sakamakon zaben 2019 tsakanin Buhari da Atiku zai kasance

‘Dan takarar wanda yanzu zai kara da gwamna Abdullahi Ganduje na APC da Buhari ya daga hannun sa a makon jiya, ya bayyana cewa gaskiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sa yake tare da shi har ya ke nema a zabe sa.

Zaura wanda yace tun kafin yayi takara yake kaunar Buhari yayi alkawarin ganin ya samu mutane sun zabi shugaban kasar domin ya zarce a kan kujerar sa. AA Zaura ya kuma bayyana manufofin sa na gyara Kano inda ya zama gwamna.

Alhaji Zaura yace idan yayi gwamna a Kano, jihar za ta koma tamkar Birnin Dubai domin zai inganta wutan lantarki kuma zai gyara sha'anin kiwon lafiya. Zaura zai fuskanci kalubale daga jam'iyyu da-dama.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel