Daga hannun Ganduje: Abokin barawo, barawo ne - Sakon Kwankwaso zuwa ga Buhari

Daga hannun Ganduje: Abokin barawo, barawo ne - Sakon Kwankwaso zuwa ga Buhari

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata dake wakiltar mazabar jihar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi tsokaci game da daga hannun Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Shugaba Muhammadu Buhari yayi.

Sanatan wanda ke zaman jagoran darikar tafiyar siyasar nan da ake yi wa lakani da Kwankwasiyya yayi wannan tsokaci ne akan maganar ranar Juma'ar da ta gabata ne a Karamar hukumar Dawakin Tofa lokacin da yake magana a gaban dumbin magoya bayan sa.

Daga hannun Ganduje: Abokin barawo, barawo ne - Sakon Kwankwaso zuwa ga Buhari

Daga hannun Ganduje: Abokin barawo, barawo ne - Sakon Kwankwaso zuwa ga Buhari
Source: Twitter

KU KARANTA: Rundunar 'yan sanda tayi babban kamu a jihar Edo

Tsohon gwamnan wanda ya nuna rashin jin dadin sa game da daga hannun Gwamnan jihar da Shugaba Buhari yayi, ya kuma fadawa magoya bayan nasa cewa abokin barawo-barawo ne.

Shi dai gwamnan na Kano yana fuskantar matsin lamba ne daga al'ummar jihar tun bayan bullar wasu fayafayan bidiyo dauke da shi yana karbar daloli yana kuma zurawa a cikin babbar rigar sa daga hannun wani dan kwangila.

A wani labarin kuma, Dan takarar gwamnan Kano a karkashin jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf ya ce ya tabbatar tsohon gwamnan jihar Rabi'u Musa Kwankwaso ba zai sa ya yi abin da ba daidai ba.

Da aka tambaye shi, shin idan Kwankwaso ya bukaci ya yi abin da ya saba wa manufofin ci gaban Kano zai bijire masa? Sai ya ce ba bijirewa zai yi ba, zai yi kokarin ganar da shi gaskiya ne ta hanyar bayani.

Ga dai bidiyon nan:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel