Samun goyon bayan kungiyar dattawan Arewa da Kudu ta farantawa Atiku

Samun goyon bayan kungiyar dattawan Arewa da Kudu ta farantawa Atiku

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu cewa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gigita cikin farin ciki sakamakon samun goyon bayan kungiyar dattawan Arewa da Kudu yayin da babban zabe ya gabato.

Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana murnar sa cikin zubar hawaye sakamakon samun goyon bayan dattawan Arewa da Kudu yayin da suka yi riko da shi a matsayin dan takarar su na zaben kujerar shugaban kasa.

Samun goyon bayan kungiyar dattawan Arewa da Kudu ta farantawa Atiku

Samun goyon bayan kungiyar dattawan Arewa da Kudu ta farantawa Atiku
Source: UGC

Ko shakka ba bu Atiku ya samu goyon bayan kungiyar Afenifere ta Yarbawa, Ndigbo ta Inyamurai, dattawan Arewa, da kuma kungiyar yankin Neja Delta. Kungiyoyin sun yi riko da shi a matsayin dan takarar su na kujerar shugaban kasa da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu.

Atiku cikin wata sanarwa a yau Lahadi da sa hannun hadimin sa akan hulda da manema labarai, Gbenga Daniel, ya ce samun wannan gagarumin goyon baya ya kara masa karfin gwiwa da kuma karsashi na jajircewa wajen cimma nasara a babban zabe domin sanya Najeriya bisa turba da tafarki madaidaici na aminci.

Yayin da ya rage sauran kwanaki 12 a gudanar da babban zabe, a yau Lahadi tsohon mataimakin shugaban kasa ya samun goyon bayan manyan kungiyoyin hudu da suka hadar da dukkanin yankuna da ke Arewa da Kudancin Najeriya.

KARANTA KUMA: Yadda sakamakon zaben 2019 tsakanin Buhari da Atiku zai kasance - Alkaluma

Atiku ya ce zai jajirce tare da tsayuwar daka na tabbatar da romon dimokuradiyya ya kwarara cikin dukkanin yankunan Najeriya bisa ga tanadi da kuma tsare-tsare na kundin tsarin mulki kamar yadda majiyar mu ta jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Yayin zayyana godiya sa marar iyaka ga kungiyoyin da suka sanya aminci a gare sa, Atiku cikin neman yarda ta Mahaliccin sa ya sha alwashin sauke nauyin da zai rataya a kansa muddin ya taki nasara a babban zaben kasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel