Rundunar soji ta kama 'yan dabar siyasa da muggan makamai, hotuna

Rundunar soji ta kama 'yan dabar siyasa da muggan makamai, hotuna

Rundunar sojin Najeriya da ke aikin atisayen rawar gansheka III da taimakon ragowar jami’an tsaro na hadin gwuiwar sun wasu ‘yan dabar siyasa da muggan makamai a jihar Sokoto.

A wani jawabi da kakakin rundunar soji, Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman, ya fitar a yau, Lahadi, ya ce an samu wasu muggan makamai irin na gargajiya tare da ‘yan dabar.

A cewar sa, tuni an tattara bayana 16 daga cikin ‘yan dabar, kuma tuni an mika su hannun jami’an rundunar ‘yan sanda domin daukan mataki nag aba.

Kazalika, ya bayyana cewar jami’an tsaro na fuskantar matsin lamaba a kan su saki ‘yan dabar.

Rundunar soji ta kama 'yan dabar siyasa da muggan makamai, hotuna

Muggan makamai
Source: Twitter

Rundunar soji ta kama 'yan dabar siyasa da muggan makamai, hotuna

Muggan makamai
Source: Twitter

A yayin da mu ke cikin gudanar da bincike a kan ‘yan dabar, fitaccen dan siyasa kuma Sanata mai ci daga jihar Sokoto ya zo wurin tare da bawa ‘yan sandan da ke tsaron lafiyar sa umarnin su saki ‘yan dabar.

DUBA WANNAN: Kamfen din APC: Mutum 2 sun mutu, da yawa sun raunata a jihar Oyo

“Daya daga cikin jami’an ‘yan sandan Sanatan har rigar jami’in DSS ya yaga a kokawar neman kwace makaman da aka samu tare da ‘yan dabar. Kazalika, wani babban dan siyasa daga jihar Zamfara ya yi kokarin an saki matasan da aka kama,” a cewar Birgediya Janar Usman.

Rundunar soji ta kama 'yan dabar siyasa da muggan makamai, hotuna

Kwayoyin maye
Source: Twitter

Rundunar soji ta kama 'yan dabar siyasa da muggan makamai, hotuna

Rundunar soji ta kama 'yan dabar siyasa da muggan makamai
Source: Twitter

Sannan ya kara da cewa, “ma su son a saki matasan ba su da wani dalili da ya wuce son zuciya, halayensu sun matukar ba mu mamaki kuma ba zamu yarda da hakan ba.”

Kakakin na rundunar soji y ace dakarun soji na yin aiki ne bias kware w aba tare da la’akari da banbanci siyasa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel