Kamfen din APC: Mutum 2 sun mutu, da yawa sun raunata a jihar Oyo

Kamfen din APC: Mutum 2 sun mutu, da yawa sun raunata a jihar Oyo

A kalla mutane biyu ne su ka rasa ran su yayin wani kazamin rikici tsakanin wasu kungiyoyi da ake zargin 'yan dabar siyasa ne a wurin taron gangamin yakin neman zaben jam'iyyar APC da aka yi a yankin Igboora da ke jihar Oyo.

Lamarin ya faru ne jim kadab bayan kammala taron yakin neman zaben jam'iyyar APC da aka yi a tashar mota da ke garin Igboora da yammacin jiya, Asabar.

An fara yakin neman zaben karkashin jagorancin gwamanan jihar Oyo, Abiola Ajimobi, cikin lumana da rangadin a sassa daban-daban kafin daga bisanai su karasa zuwa yankin Igboora.

Rahotanni sun bayyana cewar gwamna Ajimobi da dan takarar gwamanan APC a jihar Oyo, Cif Adebayo Adelabu, sun kewaya tare da nuna jin dadi ga dumbin jama'ar da su ka fito domin nuna ,a su goyon baya.

Kamfen din APC: Mutum 2 sun mutu, da yawa sun raunata a jihar Oyo

Kamfen din APC: Mutum 2 sun mutu, da yawa sun raunata a jihar Oyo
Source: Twitter

Sai dai, an sammu barkewar rikici tsakanin wasu kungiyoyin 'yan daba jim kadan bayan tawagar gwamna da dan takarar ta bar tashar motar Igboora, wurin da suka ziyarta domin gudanar da yakin neman zabe.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar daga cikin wadan da su ka mutu akwai wani dan uwa ga shugaban jam'iyyar APC a yankin Igboora, ya mutu ne bayan harsashi ya same shi yayin da ake gwanza rikin.

DUBA WANNAN: Siyasar Kano: Dalilin da ya sa ban halarci mahawarar 'yan takara ba - Ganduje

Shaidar gani da ido ya shaidawa NAN cewar rikicin ya samo asali ne bayan wata kungiyar 'yan daba ta bi bayan dan takarar gwamna domin ya ba su kudi amma sai wata kungiyar ta ;yan daba dake bin tawagar kamfen di ta hana su karasa wa wurin dan takarar gwamnan.

Tuni faruwar lamarin ta haddasa cacar baki tsakanin jam'iyyun APC sa PDP a jihar Oyo. A yayin da APC ke zargin PDP da hannu a cikin tayar da rikicin, ita kuwa PDP kira ta yi ga APC da ta fito da wadan da su ka tayar da rigimar domin a tare da jam'iyyar su ke.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel